Neman Ceto 2



Neman Ceto Daga Masu Ceto Na Gaskiya

 

Mawallafi: Ayatullahi Ja’afar Subhani

Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani

Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id

Neman ceto daga masu ceto na gaskiya wani abu ne wanda ya shahara tsakanin al’ummar musulmi tun daga zamanin Manzo har zuwa zamanin da muke a cikinsa, sannan babu wani daga cikin malaman musulunci da ya yi inkarin neman ceto daga masu ceto na gaskiya. Sai kawai mutum biyu su ne kamar haka:

1-Ibn Taimiyya a farkon karni na takwas.

2-Muhammad Bn Abdul wahab a cikin karni na sha biyu.

Dukkan wadannan mutane guda biyu sun hana neman ceto daga masu ceto na gaskiya inda suke cewa: Annabawa da waliyyai da mala’iku suna da hakkin yin ceto a ranar tashin kiyama, amma dole ne a nemi wannan ceto ga wanda yake shi ne mamallakin ceto wato Allah (s.w.t) ga abin da Ibn Taimiyya yake cewa: Ya Ubangiji, ka sanya mana annabi da sauran bayinka na gari masu ceto a gare mu ranar kiyama, don haka ba mu da damar mu ce ya Manzo ka cece mu![1] Kafin mu kawo dalilan da suke kawowa wajen hani a kan neman ceto, zamu fara kawo dalilan da suke halasta hakan daga Kur’ani da Sunna:

1-Neman Ceto Neman Addu’a Ne



1 2 3 4 5 next