Neman Ceto 2Neman ceto daga Manzo ko wani daya daga cikin manyan bayin Allah ba wani abu ne wanda ya wuce addu’a da neman gafara ba daga Allah madaukaki, sakamakon matsayin da suke da shi a wajen Allah zai sanya addu’arsu ta samu karbuwa a wajen Allah madaukaki, ta yadda mai zunubi zai samu gafarar Allah sakamakon haka. Don haka neman addu’a koda kuwa daga dan’uwa mumini ne ai ba shi da matsala ina ga ace neman addu’a daga manzon Allah. (s.a.w) Idan muna cewa: “Ya kai mai matsayi a wajen Allah, ka cece mu a wajen Allah†(wato ka nema mana Allah ya yafe mana zunubbammu). Lafazin shafa’a saudayawa ya zo a cikin hadisi da ma’anar addu’a mai yawa, haka nan marubucin Sahih Bukhari a cikin littafinsa ya kawo babi guda biyu, daya daga cikinsu yana magana ne a kan rokon musulmi daga shugaba, daya kuwa ya zo ne dangane da rokon mushrikai daga musulmi, ya yi amfani da lafazin “Shafa’a†a cikin wadannan babuka guda biyu. Wannan shi ne abin da ya kawo farkon duka babin guda biyu kamar haka: A-Idan suka nemi “shafa’a†daga shugaba don ya rokar musu ruwan sama bai kamata ba ya ki karbar rokonsuâ€. B-Idan mushrikai suka nemi “shafa’a†daga muminai yayin fari. A nan bayyane yake cewa kalmar “shafa’a†wacce take nufin ceto a nan tana bayar da ma’anar addu’a, haka hadisin da Ibn Abbas ya ruwaito daga Manzo (s.a.w) ga abin da yake cewa: “Duk lokacin da mutum ya mutu mutum arba’in daga cikin musulmai wadanda ba su shirka da Allah suka halarci jana’izarsa, sai Allah ya karbi “shafa’arsu’da suke yi masaâ€[2]. Shafa’ar wadannan mutane wadanda suka halarci jana’izarsa bai wuce addu’ar da suke yi masa ba yayin da suke masa salla suna cewa: Ya Allah ya gafarta masa! Don haka idan har ma’anar shafa’a ko ceto shi ne yi wa mutum addu’a me zai sanya ya zama haramun. 2- Hadisin Anas Da Neman Ceto Tirmizi wanda yake daya daga cikin marubutan sannan ya ruwaito hadisi daga Anass Bn Malik yana cewa: Na roki Manzo Allah cewa ya cece ni ranar kiyama, sai ya ce, zan yi hakan, sai na ce masa ina ne zan neme ka? Sai ya ce: ka neme ni a kan siradi.[3] Anass sakamakon yakininsa da matsayin Manzo ya nemi ceto daga gare shi Manzo kuma ya yi masa alkawari, sam bai zo ba ga tunanin Anass cewa wai neman ceto wani abu ne wanda yake shirka.
|