Neman Ceto



Manzo (s.a.w) yana cewa: “An ba ni abubuwa guda biya…kuma an ba ni ceto sai na yi tanadinsa ga al’umma ga duk wanda bai yi shirka da Allah baâ€‌. [14]

Sannan Manzo yana cewa: “Nine farkon wanda zan yi ceto kuma farkon wanda za a karbi cetonsaâ€‌[15].

Abu Zar yana cewa: Manzo (s.a.w) ya yi salla a wani dare, Sai ya karanta wata aya har zuwa asuba yana ruku’u da sujjada da ita, Wannan aya ita ce: “In ka yi musu azaba, lallai su bayinka ne, idan kuwa ka yi musu gafara, lallai kai mabuwayi ne mai hikimaâ€‌. Yayin da asuba ta yi sai ya ce wa Manzo (s.a.w) ba ka gushe ba kana karanta wannan aya har asubahi ta yi, kana ruku’u kana sujjada da ita, Sai ya ce: Lallai na roki Allah ta’ala ne a kan ceton al’ummata, kuma ya ba ni shi, insha Allah zata kasance ga duk wanda bai yi shirka da Allah ba a kan komai.[16]

A nan zamu takaita da wadannan ruwayoyi daga Manzo (s.a.w) a cikin tafsirin manshur Jawid wadanda muka rubuta shi ta fuskar maudu’ai na Kur’ani, muna kawo ruwayoyi fiye da dari da aka ruwaito daga Manzo da aimma (a.s) dangane da ceto, a cikin wannan littafi mun kawo sharuddan ceto da masu ceto da sharuddan wadanda za a ceta aranar kiyama da sakamakon ceton a bayyane.[17]

Kamar yadda yake kowa ya yarda da asalin ceto har kuwa da Muhammad Bn Abdul wahab [18]da malaminsa Ibn Taimiyya duk sun yarda da wannan magana, don haka a nan ba zamu tsawaita magana ba a kansa. Abin da yake muhimmi a nan shi ne, mas’la ta biyu, wacce wahabiyawa suke haramtawa, wannan kuwa shi ne neman ceto daga wadanda suka cancanci yin ceto na gaskiya.[19] Don haka a kan wannan ne zamu yi cikakken bayani a fasali mai zuwa.

Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com – www.hikima.org

Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)

Facebook: Haidar Center - December, 2012



 



back 1 2 3 4 5 6 7