Neman Ceto



B-Wasu mutane suna da hakkin yin ceto wadanda suke da wasu siffofi na musamman.

Ga matanin wadannan ayoyin kamar haka:

1-“Wa zai iya yin ceto ba tare da izininsa baâ€‌[3].

Zahirin wannan aya yana nuna cewa babu wanda zai iya yin ceto sai tare da izini daga Ubangiji, amma ta wata fuska wannan aya tana nuna mana cewa akwai wadanda zasu yi ceto a ranar kiyama tare da izinin Ubangiji.

2-“Babu wani mai ceto sai bayan izininsaâ€‌[4].

3-“Babu wanda ya mallaki ceto daga abubuwan da suke bauta wa sai wanda ya riki wani alkawari da Allahâ€‌[5].

Wato wasu ne kawai daga cikin mutane suke iya yin ceto, wato wadanda Allah ya yi wa alkawarin yin ceto, Allah madaukai zai bayar da alkawarin ceto ga wasu daga cikin wadanda ake bauta wa wato wadanda suka kadaita Allah madaukaki kamar irin annabi Isa (a.s) wanda kiristoci suke bauta wa.

4-“A wannan ranar ceto ba ya amfani sai dai wanda Allah mai rahama ya bai wa izini ya kuma yarje masa maganaâ€‌[6].

5-“Babu wanda cetonsa zai yi amfani sai wanda Allah ya bai wa iziniâ€‌[7].

 



back 1 2 3 4 5 6 7 next