Neman Ceto



Misali nufin Allah wanda yake mai hikima ya tsara cewa kwarar ni’imarsa zata biyo ne ta hanyar manzanninsa zuwa ga sauran mutane, domin babu wani mutum ban da su annabawa da ya cancanci sauraren sakon Allah kai tsaye daga gare shi.

Tare da kula da wannan babu wani abu wanda zai hana cewa kwarar ni’ima a wata duniyar ma zata kasance kamar haka bisa wannan tsari. Wato gafarar Allah zata bi ta hanyar ruhin tsarkakan bayin Allah zuwa ga bayin masu sabo wadanda suka cancanci su sami wannan falalar, kamar yadda ya ksance shiryarwar Ubangiji a wannan duniya tana biyowa ne hanyar annabawa da manzannin Allah madaukaki zuwa sauran al’umma.

Babu shakka wannan ni’aimar Ubangiji tana iya gangarowa kai tsaye daga Allah bat re da ta biyo ta hanyar wani daga cikin waliyyan Allah ba zuwa ga masu sabo da zunubi. Amma nifin Allah wanda yake cike da hikima ya yi rigaye a kan cewa wannan falala ta ruhi a waccan duniya sai ta biyo ta hannun wasu daga cikin bayin Allah masu tsarki. Amma me ya sa haka?

Wannan kuwa ya kasance domin waliyyan Allah da bayinsa na kwarai da mala’ikunsa na sama da masu daukar al-arshi, wadanda suka gabatar da dukkan rayuwarsu wajen bin Allah madaukaki, sannan ba su taba ketare iyakar Allah daga bautarsa ba, don haka sun cancanci yabo da girmamawa, daya daga cikin alamar girmamasu kuwa shi ne, karbar addu’arsu dangane da masu sabo, wannan kuwa yana kasancewa ne a cikin yanayi na musamman,

Ceton waliyyan Allah ba haka nan yake a sake ba, wato babu wani sharadi. Waliyyan Allah bazasu iya ceto ba tare da izinin Allah ba, wato ya zamana su ne suke da ikon yin hakan daga kawunansu, alhali duk al’amura a ranar kiyama suna hannun Allah, kamar yadda kowane lokaci muke karantawa a cikin sallolimmu cewa; “Shi kadai ne mai mulikin ranar sakamakoâ€‌, amma duk da haka wanda yake da wannan cikakken iko zai bai wa wasu daga cikin bayinsa izini ta yadda zasu iya gudanar da wannan aiki.

Ceto Wani Nau’i Ne Na Tsarkakewa

A mahanga Kur’ani mutuwa ba ita ce karshen rayuwa ba, mutuwa wata kofa ce domin shiga wata duniya da ake kira barzahu inda rayuwarta ta sha bamban da rayuwar wannan duniyar, yayin da wasu daga cikin mutane suna cikin azaba wasu kuwa suna cikin ni’imar Ubangiji.

Wasu gungu daga cikin masu zunubi wadanda ba su yanke alakarsu ba da imani da Allah madaukaki, sannan sun kiyaye alakarsu da masu ceto a wajen Allah, to wadanda zasu hadu da sakamakon wasu daga cikin ayyukansu a cikin rayuwar barzahu, wannan kuwa zai kasance ne a matsayin tsarkake su daga zunubban da suka aikata, wadannan mutane yayin da zasu jefa kafarsu a filin tashin kiyama, sakamkon nau’i na tsarkakewar da aka yi musu arayuwar barzahu, zasu samu cancantar samun gafarar ubangijin talikai, a mahangar wadanda suka dauki al’amarin ceton masu matsayin tabbataccen al’amari, wani abu ne na tsarkake dukkan wata sauran daudar zunubi da ta rage na masu sabo, ta yadda ruhinsu zai tsarkaka daga dukkan wata tsatsar da ta bata shi da zunubi.

Bambancin Ceto Da Kamun kafa A Rayuwar Duniya

Sakamakon wasu maganganu ya sanya wasu mutane da ba su fahimci al’amura ba, suna tunanin cewa, ceton waliyyai kamar kamun kafa da wani mutum ne a duniya wajen cimma wani abu da yake bukata, wato amfani da wanda ka sani ko nuna bambanci domin cimma wani abu, don cire wannan matsala daga kunnuwan mutane, zamu bayyanar da bambanci tsakanin ceto da kamun kafa a rayuwar duniya ta hanyoyi guda uku kamar haka:



back 1 2 3 4 5 6 7 next