Kamun kafa Da Annabawa Da Waliyan Allah 4



Wannan nau’i na tawassuli kamar wani dora nauyi ne ga Allah ta yadda dole ne Allah ya bayar da wannan hakki da ya hau kansa, alhali kuwa babu wani nauyi na wani abin halitta wanda yake a kan Allah madaukaki.

Amsa: Hakkin abin halitta a kan Allah muna iya kallon sa ta fuska biyu:

A-Sakamakon wasu ayyukana bawa yakan iya samun wani hakki a kan Allah kamar yadda mai bin bashi yake da hakki a kan wanda yake bi bashi. Irin wannan hakki ba zamu iya tunaninsa ba a kan Allah madaukaki daga bangaren bawa, domin kuwa bawan Allah bai mallaki komai ba, ta yadda ta hanyar wannan zai samu wani hakki a kan Allah.

B-Hakin da shi da kansa Allah ta hanyar wani lutfi wanda ya yi ga shi bawa, ta wannan hanyar sai bawan ya samu hakki a wajen Allah. Wato hakikanin kuwa shi ne wata falala ce wacce Allah ya yi wa bawa sakamakon haka sai ya sanya bawan yana da wani hakki a kan Allah madaukaki, ta yadda ya sanya kansa matsayin wanda ake ba shi, shi kuma bawa matsayin mai bin bashi, bayan kasantuwar cewa wannan yana iya yiwuwa a cikin Kur’ani akwai dalilai masu tabbatar mana da hakan.

Wani lokaci Allah yana daukar kansa matsayin wanda ya dauki bashi daga bayinsa, shi kuwa bawa masatyin mai ba ba bashi, a kan hakane yake cewa: “Wa zai bai wa Allah rance mai kyau”.[8]

Bayan wannan akwai ayoyi da yawa wadanda suke bayani a kan cewa sakamakon wata baiwa da Allah yake wa bayinsa, zasu kasance suna samun wani hakki na musamman ga Allah wanda yake ba shi da farko ba shi da karshe. A wasu wurare ga abin da yake cewa:

1-“Ya kasance hakki a kanmu mu taimaki muminai”[9].

2-“Alkawari ne a kan Allah kuma hakki ne a cikin Attaura da Injila”[10].

3-“Kuma hakki ne a kanmu mu taimaki muminai”[11].

4-Karbar tuba ya wajaba a kan Allah ga wadanda suke ayyuka mummuna sakamakon jahilci, sannan sai suka tuba ba tare da jinkiri ba”[12].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next