Kamun kafa Da Annabawa Da Waliyan Allah 4



Masana ruwaya sun yi hukuncin da ya dace a kansa:

Abu Hatim yana rubuta cewa: Ana iya rubuta hadisinsa.

Ibn Mu’in yana cewa: Mutumin kirki ne.

Ibn Hajar yana cewa: Mai gaskiya ne.

Ibn Adi yana cewa: Ya kasance yana ruwaito hadisi daga mutanen kirki.

Ibn Sa’ad yana cewa: Hajaj ya rubuta wa wani daga cikin hakimansa mai suna Muhammad Bn Kasim takarda cewa: Ka kama Atiyya, sannan ka bijiro masa da zagin Ali ya kara da cewa shi mutum ne amintacce sannan hadisansa ingantattu ne.

Idan har ma wasu sun kasance suna sukarsa laifinsa bai wuce shi’anci ba, shi’an da ma’anarsa shi ne son Ali da ‘ya’yansa (a.s)

Sannan yanayin wannan hadisi yana tabbatar mana cewa maganar ma’asumi ce, sannan makamantan wannan hadisi suna da yawa a musulunci.

Kamun kafa Da Manzo Da Annabawan Da Suka Gabata

Dabarani a cikin mu’ujam dinsa, ya ruwaito hadisi tare da dangane daga Anass Bn Malik yana cewa: lokacin da Fadima bnt Asad ta rasu, Manzo ya halarci gadon mutuwarta, sai ya ce: Ya Allah ka yi wa mamata ta biyu rahama, kin kasance kina jin yunwa kina kosar da ni, kin kasance kina rasa sutura kina suturta ni, kinkasance kina kin cin abin ci mai dadi ni kuwa ki ba ni mai dadi, ba ki da wata manufa a cikin wannan aiki sai neman yardar Allah.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next