Kamun kafa Da Annabawa Da Waliyan Allah 4



5-Wafa’ul wafa li’akhabari daril Mustafa, wanda Sayyid Nuruddin samhudi ya rubuta, (ya rasu shekara ta 911) ya yi Bahasi a kan Tawassuli a cikin juz’i na hudu na wannan littafi.

6-Al-mawahibud daniyya wanda Abu Abbas kustalani (ya rasu a shekara 933) ya yi bahsin Tawassuli a cikin wannan littafi nasa.

7-Sharhul mawahibud diniyya, wanda Misri zarkani ya rubuta, (ya rasu a shekara ta 1122) ya yimaganar Tawassuli a cikin mujalladi na takwas.

8-Sulhul Ikhwan: Wanda Khalidi Bagdadi ya rubuta, (ya rasu a shekara ta 1299) a cikin wannan littafi ya rubuta risala ta musamman raddi a kan Alusi bayan rasuwarsa a shekara ta 1306 a ka buga littafin.

9-Kanzul matalib: wanda Adwi Ahmzawi ya rubuta, (ya rasu shekara ta1303).

10-Furkanul kur’an wanda Izami shafi’i ya rbuta.

Amma ta bangaren Shi’a an rubuta littafai masu yawa a kan haka, a nan kawai zamu kawo wasu daga cikinsu kamar haka:

1-Sabilur rashad liman aradas sadad, wanda sheikh Ja’afar Kashiful Gida ya rubuta, (ya rasu 1227) an buga wannan littafi saudayawa.

2-Kashful irtiyab, wanda Sayyid Jabalil Amuli ya rubuta, (1282-1373).

3-Al-gadir, Allama Amini ya yi Bahasi mai tsawo a kan wannan magana.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next