Kamun kafa Da Annabawa Da Waliyan Allah 4Kamun kafa Da Annabawa Da Waliyan Allah 4 Mawallafi: Ayatullahi Ja’afar Subhani Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id Tarihin Kamun kafa Da Bayin Allah Tsarkaka Tarihi a bayyane yana nuna cewa tun kafin zuwan musulunci mutane masu kadaita Allah sun kasance suna Kamun kafa da wadanda suke ganin suna da matsayi a wurin Allah, sannan kuma sakamakon tsarkin fidirarsu su suna ganin wannan aiki wani aiki ne wanda yake mai kyau. A nan zamu yi nuni da wasu daga cikinsu: 1-Abdul Mutallib da kamun kafa da Muhammad (s.a.w) a lokacin da yake shan nono, tsananin fari ya mamaye Makka da kewayenta, sai Abdul mutallib ya dauki jikansa mai shan nono ya daga sama, sannan ya roki Allah ruwan sama, har ana cewa mashahuriyar wakar Abu Dalib ya yi ta ne dangane da haka wacce take cewa: Fuska mai haske wacce gizagizai suka yi ruwa dominta, wacce sakamakon haka ne marayu da mata gwagware suka samu mafaka. 2-Abu Dalib da kamun kafa da Manzo a lokacin da yake saurayi Kamar abin da ya faru lokacin Abdul mutallib a lokacin shugabancin Abu Dalib ma ya sake faruwa, sakamakon haka ne sai kuraishawa suka zo wajensa suka kawo masa kuka a kan fari da rashin ruwa da ake ciki, Sai Abu Dalib ya yanke shawara a inda ya roki Allah da ya saukar musu da ruwa tare da kamun kafa da dan dan’uwansa Muhammad wanda yake karamin yaro ne a wannan lokaci. Sai ya kama hannun Manzo ya jingina bayansa ga dakin ka’aba, wani lokaci yana nuni da wannan yaro wani lokaci kuwa yana nuni da sama, wato Ubangiji albarkacin wannan yaro ka saukar mana da rahamarka. Ba tare da tsawaita lokaci ba, sai hadari ya mamaye garin Makka da kewayanta, sai koramu da tabkuna suka cika makil da ruwa[1].
|