Ziyarar Kaburbura Masu Daraja Kai asali ma ziyarar kaburbura wani darasi ne kuma mai sanya mutum ya rika tunawa da lahira wanda kuma ya kunshi karantawa wadanda aka ziyarta fatiha. Ta yaya za a hana mata dangane da samun wannan falala? Da wani kalamin kasantuwar hikimar ziyarar kaburbura tana kunshe da daukar darasi da tunawa da lahira, ta yaya za a kebance maza kawai ban da mata a ciki? Kasantuwar ziyarar kaburbura ya nisanta da duk wani sabo, idan muka dauka haka kuma sai aka hana mata a wancan lokaci, to kila sakamakon cewa ba su kiyaye sharuddan da suka kamata ne. Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com – www.hikima.org – www.haidarcip.org Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP) Facebook: Haidar Center - December, 2012 |