Ziyarar Kaburbura Masu Daraja



Suka ce: A’a.

Ya ce: zaku saka gawar kabari ne?

Suka ce: A’a.

Sai Manzo ya ce: ku koma gida kuma su masu sabo ne ba masu neman lada ba.

Amsa:

 Wannan hadisi ta fuskar ma’ana da isnadi ba a bin dogaro ba ne da za a iya kafa hujja da shi, saboda sanadin wannan hadisi (maruwaita hadisin) akwai Dinar Bn Amru ya shiga a cikinsu, ta fuskar masu ilimin ruwaya suna cewa ba a san shi ba, kuma mutum ne mai karya mai sabo kuma wanda ake bari.

 Shin ana iya dogara wajen kafa hujja da irin wannan hadisi wanda maruwaicinsa yake da wadannan siffofi na rauni?

Mu dauka ma dangane wannan hadisi yana da inganci, sam ba shi da alaka da ziyarar kabari, domin kuwa Allah wadai din da Manzo ya yi ya shafi matan da suka fito domin kallon janaza, ba tare da wani aiki da zasu yi ba wajen kai jana’zar. Saboda haka wannan bai shafi batun ziyarar kaburbura ba.

 A nan dole mu yi tunatar wa akan wani al’amari shi ne, addinin musulunci addini ne wanda ya dace da halitta mutum, kuma mai sauki, Manzo yana cewa: “Akidun musulunci akidu ne tabbatattu duk wanda zai shiga cikinsu ya shiga tare da dalilai na hankali”.

 Mu dauka cewa mahaifiyar mumini sai ta rasa danta aka kuma rufe shi a karkashin kasa, sai ta damu a kan hakan, abin da kawai zata iya yi a nan shi ne ta ziyarci kabarinsa. A nan idan aka hana ta yin wannan aiki wanda ya dace da hankali kuma dukkan mutanen duniya sun tafi a kan hakan, wannan zai haifar da muguwar damuwa ga zuciyar uwa. Shin musulunci zai yi hani da irin wannan aiki sannan kuma ya zama addini mai sauki?



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 next