Ziyarar Kaburbura Masu Daraja



Mawallafi: Ayatullahi Ja’afar Subhani

Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani

Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id

[Al’adar Mutunce Kuma Sunnar Ubangiji]

Makabarta wani wuri ne babba a cikin birni da kauye inda yake dauke da babba da yaro mai iko da talaka daga magabata wadanda suke cikin barci mai zurfi wanda kamar ba za a farka ba.

 Ziyartar wannan wuri Wanda yake nuna gajiyawar dan Adam, sannan yana da rawar da yake takawa wajen gusar da duk nuna iko ko kwadayin abin duniya ga mutum. Mutum mai hankali yayin da ya ga wannan wuri mai ban tsoro, zai fahimci rashin tabbatuwar duniya daga kusa, sannan ya fara tunani akan mafita sakamkon fahimtar manufar halittar duniya da ya yi zai sanya ya fita daga cikin magagin dimuwa da son kai, sannan ya fara tunanin neman abin zai taimaka masa wajen rayuwar da ba ta da iyaka. Manzo (s.a.w) a kan wannan al’amari domin tarbiyyantar da al’umma yana cewa: “Ku ziyarci kaburbura domin zasu tuna muku ranar karshe”.[1] Sannan a wani wurin daban yana cewa: “Ku ziyarci makabarta domin kuwa akwai darasi gareku a cikin yin hakan”.[2]

 Sannan akwai wasu daga cikin mawakan zamani kamar Marigayi Sayyid Sadik Sarmad yayin ziyarar Kasar misra da kuma ziyarar Kaburburan fir’aunoni, sai ya yi wata a kan haka wadda take fassara hadisin Manzo (s.a.w) a kan hakan:

Ziyartar Kaburburan Masoya

 Mutanen da suka rasa wani masoyinsu sakamakon alaka ta jini da soyayyar da take tsakaninsu ba zasu manta da shi ba, zaka ga kodayaushe suna yin taruka domin tunawa da shi sannan suna yin kokari wajen girmama shi. Yayin da mutuwa ta kare su daga saduwa ta jiki, sai suka koma bangaren guda wato ta hanyar ruhi suna saduwa da shi, don haka ne zaka ga suna zuwa wurin da aka rufe shi ta hanyar daidaiku da cikin jama’a domin su ziyarce shi sannan suna yin taruka domin tunawa da shi din. Taron mutuwa da ziyartar kaburburan wadan suka rasu wata al’ada ce wadda ta hade ko’ina a cikin al’ummar duniya, ta haka ne zamu iya cewa wannan al’amari yana da alaka da halittar mutum. Sakamkon soyayyar da take tsakanin mutane da danginsu wadda take janyo su da su zo domin su ziyarce su yayin da suke da rai, wannan shi yake janyo su ziyarci kaburansu yayin da ba su da rai. Musamman kamar yadda yake a musulunci cewa ruhin mutum sabanin jikinsa ba ya lalacewa. Ba ma haka ba kawai yakan kara samun karfi na musamman a wannan duniyar sannan yana jin dadin kulawar da masoya suke yi masa ta hanyar ziyartarsa da yi masa addu’a kamar karanta masa fatiha da makamantanta, ta yadda suke kara masa nishadi da karfi.

 Don haka bai dace ba mu sha kan mutanen a kan gudanar da irin wannan al’ada wadda take wani nau’in halittar mutum ce, Abin da ya kamata shi ne mu nuna musu yadda ya kamata su aiwatar da hakan, ta yadda sakamakon soyayya ga masoyansu kada su kai zuwa ga sabon Ubangiji.



1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 next