Bincike Kan Addini



1-      Usuluddini: su ne asasi tabbatattu da ba sa sabawa komai sabawar al’ummu kamar Tauhidi da Adalci da Annabci da Makoma. Wadannan su ne shika-shikan addini.

2-      Furu’uddini: su ne janibin shari’a, wanda yake kunshe da koyarwa, kuma da kyawawan dabi’u da suka zo domin maslahar mutum da al’umma gaba daya da kuma rabautar duniya da lahira, bai kebanta da wasu jama’a ba su kadai. Wadannan su ne rassan al’amuran addini[11].

Shika-shikan Addini

Kamar yadda aka sani cewa addini yana da jiga-jigai da kuma rassan al’amuransa. Asasi ko ginshiki yana nufin doka da ka’idar da addini ya doru a kanta, ana cewa da tauhidi da adalci, da annabci, da imamanci, da makoma ranar lahira, wato: shika-shikan addini.

Zai iya yiwuwa a wajenmu bahasin imamanci ya shiga karkashin annabci, kamar yadda adalci yake shiga karkashin bahasin tauhidi, sai su koma guda uku: Tauhidi Da Annabci Da Makoma.

Yana wajaba a kan kowane baligi ya san shika-shikan addini da bayanansu.

Musulmi da Musulunci

A bisa abin da yake saukakke daga Allah madaukaki shi ne cewa “Addini a wajan Allah kawai shi ne musulunci”, wanda yake shi ne Shari’ar Ubangiji ta gaskiya wacce take Shari’ar karshe, mafi kamala da dacewa ga rabautar dan Adam, wacce ta fi kunsar maslaharsu ta duniya da lahira, mai dacewa da wanzuwa, wacce ba ta canjawa ba ta sakewa, mai kunshe da dukkan abin da dan Adam yake bukata daga tsarin rayuwar mutum da jama’a.

Kuma tun da ita wannan shari’ar ita ce ta karshe to babu makawa wata rana ta zo da Addinin musulunci zai yi karfi har ya game rayuwa da adalcinsa da dokokinsa. Wannan kuwa alkawari ne da Allah ya yi shi a cikin littattafansa.

Sannan tun da wannan addini na musulunci shi ne mafi kamala da dacewa da rayuwar dan Adam, lallai da an dabbaka shi kamar yadda ya dace, da aminci da rabauta sun mamaye ‘yan Adam, da sun kai kololuwar abin da suke mafarkinsa na yalwa, da walwala, da izza, da annashuwa, da kyawawan dabi’u, kuma da zalunci ya kau daga duniya, soyayya da ‘yan’uwantaka sun yadu a tsakanin mutane, talauci da fatara sun kau gaba daya.

Idan a yau muna ganin halin ban kunya da kaskanci da ya samu wadanda suke kiran kansu musulmi, to domin ba a aiwatar da addinin musulunci ba ne a bisa hakika kamar yadda yake a nassinsa da ruhinsa suke tun daga karni na farko.

Sai kangare wa koyarwar musulunci, da tozarta dokokinsa, da yaduwar zalunci, da ketare haddi daga bangaren Sarakunansu da talakawansu, da kebantattu da kuma baki dayansu suka kawo kaskanci ga musulmi da lahanta yunkurin ci gabansu, da raunana karfinsu, da ruguza tsarkin ruhinsu. Allah madaukaki yana cewa:



back 1 2 3 4 5 6 next