Bincike Kan AddiniKur’ani mai girma yana siffanta irin wadannan mutane da su ne mafi bata daga dabbobi: “Mun sanya wa jahannama dayawa daga aljnu da mutane da suke da zuciya da ba sa tunani da ita, da kuma idanu da ba sa gani da su, da kunnuwa da ba sa ji da su, wadannan kamar dabbobi suke, kai sun fi dabbobi bacewa, kuma wadannan su ne gafalalluâ€[7]. Ina karawa da cewa; duba ga irin wadannan fa’idoji da addini yake da shi imani da mahalicci da aiki da hakan koda an kaddara da cewar babu shi ya fi zama abin hankalta a kan rashin yarda da hakan, domin idan an koma masa; idan an kaddara babu shi to da mu da wadanda ba su yi imani da shi ba mun zama daya, amma idan akwai shi fa! kenan mun tsira su kuma sun halaka. Musulunci yana da ma’ana biyu; ma’ana mai fadi da ma’ana kebantacciya kamar haka; Ma’ana mafi fadi ; Shi ne karkata da mika wuya zuwa ga Allah da abin da ya saukar na shir’a da hukunce-hukunce. Allah madaukaki ya ce: “Kawai addini a wajan Allah shi ne muslunciâ€[8]. Musulmi shi ne wanda ya mika wuya ga abin da aka saukar na shari’a daga Allah, saboda haka akwai musulunci tun lokacin annabi Adam (a.s) da Nuhu da Ibrahim da Musa da Isa (a.s) da kuma cikon manzanni da annabawa Muhammad (s.a.w). Ma’ana kebantacciya: Shi ne addinin da manzo Muhammad Dan Abdullahi (s.a.w) ya zo da shi, muslmi shi ne wanda ya yi furuci da harshe yana mai cewa; “Na shaida babu abin bautawa sai Allah, kuma na shaida Muhammad manzon Allah neâ€. Ana kiran wannan da kalmar shahada da take kunshe da shaidawa biyu. Don haka sakamakon wannan furuci yana tilasta rashin musun duk wani abu laruri na akidar musulunci da huknce-hukuncensa, da kuma rashin musun annabtar annabawa da suka rigaya suka gabata da aka ambace su a kur’ani mai girma, wato kada ya yi musum wani abu da musulmi suka hadu a kansa gaba daya kamar wajabcin salla da azumi da hajji, da haramcin shan giya da cin riba, da sauransu. Musulunci tsarkakakke shi ne cikon addinai, domin shi ne mafi kamala da cika wanda ya zo daga Allah da ake bukatar mutum ya mika wuya zuwa gareshi[9]. Saboda haka ne ma ba a karbar wani addini sai shi: “Duk wanda ya nemi wani addini ba musulunci ba, ba za a karba daga gareshi ba, kuma shi a lahira yana cikin masu hasaraâ€[10]. Usuluddin Da Furu’arsa
Addinin musulunci addini ne na duniya gaba daya da ya game komai, kuma yana dogara bisa rukuni biyu ne na asasi:
|