Tarihin Mace A Al'adu



Misalin dokokin mace a addini Hindu: A addinin Hindu a Littafinsu na dokokin addini mai suna “Manu Dhrama Sastra” a Babin bayani game da mace ya zo cewa:

Dole ne mace ta zama ba ta da zabi a kan kanta ko yarinya ce, ko tsohuwa, ‘ya ta ubanta ce, kuma mata ta mijinta ce, uwar marayu tana karkashin ‘ya’yanta ne. Mace ba ta isa ta ci gashin kanta ba har abada, kuma dole ta yarda da wanda babanta ya zaba mijinta har abada, ta yi wa miji hidima har mutuwa kuma ba ta isa ta yi wani miji ba idan ya mutu ko ta yi tunanin wani miji bayan mutuwarsa, kuma dole ne yayin nan ta bar duk wani abu da take marmari ko kwadayi na ci mai dadi ko tufafi mai kyau da duk wani ado har rayuwarta ta kare, idan mijinta ba ya son ta yana bin wata matar kada ta sake ta ji haushi kuma ba ta da ikon takaita masa hidima da neman yardarsa. Aljannarta tana karkashin mijinta kada ta yi wani abu sai da yardarsa[9]. Uban yarinya kada ya ci sadaki ko yaya daga ciki, in ko ya yi haka daidai yake da wanda ya sayar da ita.

Duba ku ga yadda mace ba ta da ikon tunani ko sanya mai kyau ko cin abin da take marmari ko aure don mijinta ya mutu, wato da ana an gwanci ya mutu shi ke nan ta gama aure har ta mutu koda ko za ta shekara dari a Duniya, sannan kuma ba ta da ikon tunani a kan makomarta.

Mace A Al’ummu Masu Dokoki Da Cigaba

Al’ummu masu cigaba da dokoki game da abin da ya shafi mace kamar Kaldaniyawa da Rumawa da Yunaniyawa wato Girika, ba su tsira daga irin wannan ba, saboda haka zamu yi kokari mu kawo misalai game da wasu daga cikin irin wadannan al’ummu.

Mace A Gun Kaldaniyawa

A littafin Kaldniyawa na shari’a mai suna “Hamurabi” sun kafa dokar bin mace ga miji da rashin ‘yancinta faufau har ma a cikin nufi, da irada, da aiki, da bukata, kai har idan da zata saba masa ko ta yi wani abu na kashin kanta, to yana da hakkin fitar da ita daga gidansa ko ya yi mata kishiya ita kuma ya yi mu’amala da ita a matsayin baiwa, haka ma da zata yi barna koda ta abinci ce yana iya kaita kotu, idan kotu ta tabbatar da haka to za a nutsar da ita a ruwa har mutuwa. Wannan shi ne hukuncin mai barnar abincin mijinta, malam duba hukuncin barnar abinci gun Kaldaniyawa[10].

Mace A Gun Rumawa

Amma Rumawa suna daga cikin al’ummar da ta dade da kafa dokokin zamantakewa tun shekaru 400 kafin haihuwar Annabi Isa (A.S). A wajansu mai gida shi ne Ubangijin gida da matan zasu bauta masa kamar bayinsa, kuma yana da cikakken zabi, wato ba ya shawara da mace sam domin ita ribar kafa ce ta zamantakewa kawai da duk abin da ya ga dama shi zai yi, yana iya kashe matarsa da ‘ya’yansa mata idan yana ganin maslahar hakan, kuma ba mai ganin ya yi wani laifi, mata, da ‘ya, da ‘yar’uwa, duk suna cikin mawuyacin hali.

Har a Falsafarsu ba a ganin mace wani bangare na al’umma, ba a zartar da cinikinsu ko alkawarinsu ko wani abu nasu, ba su da hakkin zabe, ko wasa, kai komai ma, amma ‘ya’ya maza koda na tabanni ne suna da daraja domin suna maza, kuma idan mace ba ta haihuwa miji yana iya kashe ta saboda ba ta kawo ‘ya’ya maza a al’umma, amma idan namiji ya gane shi ne ba ya haihuwa yana iya bayar da aron matarsa ga wani dan’uwansa, idan ta yi ciki ta haihu kuma da namiji sai ya yi alfahari ya samu da.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next