Tarihin Mace A Al'adu“Na yi imani da cewa a gabanmu babu wani zabi face kara samun masaniya game da duniyar musulmi matukar muna nufin yin aiki don kare hakkin dan Adam da Dimokradiyya. Babban dalilin son sanin musulunci da fahimtar wadatacciyar wayewarsa ya samo asali ne daga kasancewarmu cikin wani addini da ba shi ba. Hakika kuwa malama Shamel ta fadaka da wannan bukatar, kuma ina fata ya zama sauran mutane su ma suna jin hakan, kuma Anamari Shamel ta share mana fagen binciken addinin musulunciâ€. Duk da an samu yardar `yan siyasa da wayayyu daga ma’abota tunani, da masana kasashen musulmi da al’adun musulunci, da ma’abuta fanni da adabi a kasar Jamus wadda ake dauka daga cikin manyan daulolin duniya a tarihin wannan zamani namu, amma sai da aka samu rikici a kan bayar da kyautar zaman lafiya a kasar Jamus ga masaniyar kasashe da al’adun musulmi (Shamel) a shekara ta 1995, tare da yardar da nasarar bangaren Shamel wato masu kira zuwa a fahimci musulunci a bisa hakikaninsa don shata matsaya suka samu. Daga cikin wadanda suke sahun gaba kuwa har da manazarta da ‘yan siyasa, da kuma shugaban kasar Jamus wanda muka kawo muhimman zantuttukansa, wannan kuwa wani abu ne mai girma da yake wuyan musulmi marubuci, kamar yadda yake a wuyan cibiyoyi da malaman Addini. Kuma musulunci addini ne da duk yadda mai kinsa ya kai da gaba da shi, to ba wani abu ba ne mai wahala ya karbe shi idan ya saurara da kyakkyawar niyya, duba fadinsa madaukaki: “Ku tafi zuwa ga Fir’auna don kuwa hakika ya yi girman kai. Sannan ku gaya masa magana mai taushi, ko zai karbi gargadi ko kuma ya ji tsoron (azabar Allah)â€[28]. Daga nan za mu fahimci cewa Kur’ani yana horon masu kira zuwa ga musulunci da su kare tunaninsa, kuma su yi magana mai taushi hatta ga wadanda suka fi kowa adawa da tsanantawa da kin imani, kuma kar su fada tarkon yanke kauna har su rufe kofar yin muhawara da tattaunawa, domin yanayi da halayen da dabi’ar abokan muhawara yana sassabawa daga marhala zuwa wata, kuma daga wani yanayi na zamantakewa da al’adu ko tarihi zuwa wani, domin saudayawa abin da aka ki karba a yau aka karbe shi a gobe, kuma abin da aka ki yarda da shi ta wannan hanya ana yarda da shi ta wata hanyar. Mace A Mahangar Musulunci
Mahangar musulunci ta girgiza duniya a wancan zamani da ta shelanta cewa; babu bambanci tsakanin mace da namiji sai da tsoron Allah a daidai wannan lokaci a duk fadin duniya daga gabas har yamma babu inda mace take da wata kima ko wani hakki muhimmi a cikin al’ummarta. Haka nan ya zo a Kur’ani mai girma fadin Allah madaukaki: “Ya ku mutane! mu mun halicce ku maza da mata… mafi girmanku a wajan Allah shi ne mafi tsoronku gare shi...â€.[29] Mace da namiji a musulunci duk daya ne sai dai a ayyuka da Allah ya bambanta su daidai gwargwadon yadda dabi’ar halittarsu take, amma ta bangaren ruhinsu babu bambanci tsakanin mace da namiji, bambancin ya shafi bangaren jiki ne, shi ya sa a maganar zamantakewar aure mace ba ta da ikon fita waje in dai ba da izinin miji ba, sai kuma lalura kamar ciwo, ko fita ta wajibi kamar neman ilimi da makamantan wannan. Haka nan musulunci ya duba maslaha a cikin dokokinsa; misali a hukuncin gado musulunci ya kiyaye masalahar duka ne domin dukiyar miji tana komawa kan matarsa da ‘ya’yansa ne, amma ta mace ta kebanta da ita ne, kuma bai wajabta mata yaki ba sai ya wajabta shi a kan namiji, haka nan ciyarwa tana kan namiji ne, amma ba a taba jin wani ya ce an zalunci shi namijin ba daga masu son sukan Addini madaukaki na musulunci wadanda ba su fahimci hakikanin dan Adam da sirrin halittarsa ba. Matsalar kasashen Musulmi Ta Al’ada Ce
Matsalar da take faruwa a kasashen musulmi ta al’ada ce ba musulunci ba, misali a wasu wurare idan mace ta yi zina aibi ne da gori ga ‘ya’yanta, sabanin namiji. Haka ma auren dole ba kasafai a kan yi wa namiji ba, amma mace da yawa ya kan faru a kanta, wannan kuwa yana komawa al’adu ne ba musulunci ba. Amma a mahanga ta musulunci duk wanda ya yi laifi shi mai zunubi ne, kuma ya yi abin kunya, ba bambanci tsakanin namiji da mace, haka nan a nufi da hakkin zabi musulunci bai bambanta namiji da mace ba. Musulunci ya daidaita mace da namiji a irada, da iko, da mallaka, da girmamawa, da rike mukami, da kasuwanci, da ibada, da Ilimi, da hankali, da hakkoki, sai ya kebance namiji da wani abu kamar iko a gida da shugabancin iyalinsa, kamar yadda ya kebance ta da hakkin renon danta da shayar da shi, da alfahari, amma da sharadin ya zama gaskiya take fada kamar maganar da take nuna tana alfahari da cewa tana da matsayi da kima gun mijinta. Amma namiji waje daya ne ya halatta ya yi takama da alfahari wato a wajan yaki a gaban makiya, kamar ya yi wa kansa kirari.
|