Tarihin Mace A Al'adu Ya kamata ne mu yi bincike a kan dokokin musulunci wanda yana da mas’aloli sama da dubu dari da ishirin da hudu, da tunani cikin irin maslahar da take kunshe a cikinsa ga rayuwar dan Adam da hikimar Allah a ciki, ta nan ne za mu iya gane kiyaye hakki da matsayi da suka shafi mace da babu kamarsa a wani Addini. Dokokin ‘yan’adamtaka da suke kunshe cikin musulunci ba a iya samun irinsu a wani addini, misali; wane Addini ne ya zo da cewa mace ita take da iko ta aurar da kanta ga wanda take so in banda Musulunci, shi ya sa ma aka shardanta yardarta ba ta wani ba, kuma ita ce zata ce: “Na aurar da kainaâ€[30]. Haka nan tana iya shardanta wa mijin cewa a saki idan ta ga dama tana da hakkin sakin kanta[31], kuma tana da hakkin yin aiki idan bai sabawa hakkinsa ba kamar likitanci, da injiniyanci, da kasuwanci, kuma tana iya rike duk wani mukami da ake da shi a kasa. Saboda haka wane Addini ne yake da nazari mai cike da kamala da kula da hakki na mace kamar musulunci? Idan da za ka duba a aikace zaka ga cewa yawancin addinai sun kasa aiki da nazarinsu kan rayuwa, amma musulunci shi ne addini da zai aikatu a aikace kuma ya kai dan Adam ga kamala babu bambantawa namiji ne shi ko mace. Musulunci yana kiyaye maslaha ne na dukkan bangaren mata da maza a dokokinsa, misalin dokar halarcin auren mace sama da daya, da babu wannan doka da mata sun samu kunci a cikin rayuwa kamar maza, kuma da an sami yaduwar fasadi mai yawa a kasashe. Shari’a ta sanya dokokin daidai da dabi’ar kowanne, misalin saki a bisa ka’ida ta farko yana hannun namiji ne sai dai idan da sharadi tsakaninsu na cewa tana iya sakin kanta[32], saboda mace idan ta fusata tana da saurin yanke hukunci, saboda haka don maslaha sai musulunci ya sanya irin wannan abubuwa a hannun namiji, shi ya sanya saudayawa ka kan ji mace ta ce ka sake ni mana amma namiji ya fita sha’anin wannan maganar domin ya san tana cikin fushi ne, da zata sauko, da a ce an sake ta din wannan yana iya jawo mata bakin ciki da ba zata taba mantawa da shi ba musamman idan tana da ‘ya’ya. Haka ne musulunci ya gina dokokinsa bisa hikima da maslaha domin cimma hadafi na gina al’umma ta gari mai iya isa zuwa kamala da Allah ya ke so ta kai zuwa gare ta. Mace Da Wasu Al’adun Musulmi
Da musulmi sun kiyaye Addininsu kamar yadda Allah ya saukar da shi da ba su samu kunci ba a kan aiki da Addininsu ba ko sau daya, Allah (S.W.T) yana cewa: “Ba a sanya muku wani kunci ba a cikin Addiniâ€[33], amma duba ka ga abin da nisantar Addinin ya janyo wa Duniyar musulmi. A nan zan kawo wasu misalai ne na kuntata wa kai da al’umma take jefa kanta a ciki ta hanyar sabawa takalifin da Allah ya dora mata da daukar sabanin hakan a matsayin addini, ko kuma riko da wasu al’adu. A irin wadannan misalai kana iya ganin yadda musulmi suka sha bamban da koyarwar msulunci ta ainihi kuma suka yi hannun riga da dokokinsa ingantattu sakamkon kaucewa wasiyyar Annabin rahama da suka yi ta biyayya ga littafin Allah da Ahlul Bait (A.S). Misali na daya: Wani abin tausayi na wani abu da ya faru sakamakon jahilci da al’adu da abokina ya ba mu labari yana mai cewa: A wani watan Ramadan mai tsananin zafi, ga rana, akwai wata mata da ta haihu daga danginsu, sai dattijon gidansu ya hana a ba ta abinci da ruwa, ya ce: Duk wanda ya ba ta ruwa Allah ya tsine masa! wai tana cikin watan azumi ne, alhalin ga shi ta haihu. Ya ce: Tana ihu tana cewa: A ba ni ruwa! Wuta ce a cikina!! Ya ce: Da magariba ta yi aka ba ta ruwa, yana ratsa makogaronta sai ta fadi sumammiya kuma ta dade ba ta motsa ba. Misali na biyu: Haka nan na yi tafiya a 1993-4 a kan hanya na ga abin tausayi, ga tsananin zafi a wani watan azumi, a cikin motarmu akwai wata mata mai shayarwa tana da jariri, nonon da zata ba shi ya yi karanci sabaoda yunwa da kishirwa da suke tare da ita, ga danta yana ta kuka. Sai na ce: Ai kuwa na ji wani malami yana cewa: Idan mace ta kai wannan hali tana iya sha don danta. A nan ne wani makiyayi dattijo da dansa rike da sanduna a kujerar gabana suka waiwayo, idanuwan nan sun yi ja kamar yana shirin cira sanda ya buga mini, yana magana da kausasawa da musuntawa, sai idanuna suka cika da hawaye saboda tausayi. Tsohon nan da mutanen cikin mota sai daka mata tsawa suke yi wai ta lallashe shi ya yi shuru! shi kuwa yaro yana ta kuka, ba nono sai dai ta ba shi ruwa, su kansu ruwan da na taba jarkar da karen motar ya mika mata don ta ba wa yaron sun yi zafi sosai. Na san ni matafi yi ne idan na yi azumi bai yi ba domin ina bin tafarkin Ahlul Baiti (A.S) ne, kuma na ga zan iya shan ruwa domin ba kodayaushe ne nake zama akwai mutane ba, ga shi kuma na yi ta fiya ta halal kafin rana ta karkata[34]. Da Azahar aka sauka salla na kewaya da tulun kasa dan karami, cike da ruwa don kama ruwa, na sha rabi na yi tsarki da rabi, na koma na karo domin in sha sai na hango matan nan a mota tana ta jijjiga yaron nan, sai tausayi ya sake kama ni, haka nan aka jahilci Addini aka cutar da mata da yara. Misali na uku: A shekarar 1990 ne a wani wata mai albarka na azumi ne na wata yarinya ce da take neman wani gida, sai na kawo ta wani waje da aka samu wani ya san gidan, amma zata dan jira kadan. Yarinyar ta kasance tana lumfashi daidai saboda zafi da wahalar tafiya, tana mai kakaro yawo fari fat tana tofarwa, tana tsaye sai ta kusa faduwa. Da aka tambaye ta sai ta ce azumi ne ya wahalar da ita. Sai na ce: Don Allah ku ba ta ruwa ta sha don ko ba komai ita matafiyiya ce babu wajabci a kanta. Sai wani cikin fushi ya ce: Sai dai kai ka ba ta, wani ma mamaki yake da ni ma’abocin addini da na san hukuncinsa amma zan ce a ba ta ruwa! Irin wadannan misalai suna da yawa a kowane bangare na rayuwar musulmi da ya hada da cinikayya, da zamantakewar al’umma, da ibada, da tattalin arziki, da siyasa. Yawancin irin wannan a kasashen musulmi yana tasowa ne daga rashin sanin musulunci da hukunce-hukuncensa ko kuma cakuda shi da al’adu, shi ya sa ma ba ya shafar mace kawai har ma da namiji. Al’ummarmu tana da bukatar ta mike ta san hukuncin addini kamar yadda Allah ya aiko Manzo (S.A.W) da shi, wannan kuwa yana bukatar jan aiki a kan malamai kuma da ita al’ummar.
|