Tarihin Mace A Al'aduHaka nan maza su ne kawai al’umma, shi ya sa gidan da babu maza hukuncinsa a rusa shi, don haka idan wani ya ga ba ya haihuwa to dole ya ba da aron matarsa don a yi mata ciki a samu namiji, in ba a samu namiji ba sai ya yi tabanni da dan wani ko dan zina ko da kuwa ta hanyar runton da ne da jayayya. Saki da aure a wajensu iri daya ne da na Rumawa, kuma ka Mace A Gun Yahudawa
Yahudawa suna da dokoki wadanda ba su dace da kima da matsayin mace ba, da kuma danne hakkin nufi na dan Adam. A dokokinsu idan da namiji zai auri yarinya, sai ya yi da’awar ya same ta ba budurwa ba, to babanta yana iya kai jini a kyalle kutu ya ce: An yi wa ‘yarsa kazafi, idan ya ci galaba sai a ci mijin tarar azurfa dari, kuma bai isa ya sake ta ba har abada, amma idan aka tabbatar da haka, to ita kam za a kai ta bayan gari ne a jefeta har mutuwa. Duba ka ga ni babu shaida, babu ikirari daga gareta, amma ana iya kashe ta. Wata tambayar ita ce, yaya aka yi uban ya samo jinin budurcinta? Daga ina kuma za a iya tabbatar da haka ko na rago ne! Haka nan suka ce: Idan mutum ya saki matarsa, ta auri wani shi ma ya sake ta, to na farkon ba shi da ikon sake aurenta domin an najasta ta, abin mamakin a nan yaya aka yi aka najasta ta, ta zama najasar da ba zata iya komawa ga na farkon ba! haka nan yaya maganar idda? A wata dokar suna cewa ne: Idan dan’uwa ya zauna da matarsa da dan’uwansa a gida daya, sai shi mijin ya mutu, to ya zama dole kan dan’uwansa ya aure ta, idan kuwa ya ki, sai ta kama hannunsa ta kai shi gaban dattijan gari ko yanki, ta cire takalminsa, ta kuma tofa masa yawu a fuska, sannan a rika kiransa da sunan: mai tubabben takalma. Tambaya ita ce: Don me ba za a Haka nan game da mata da yara duk da sun hukunta cewa ba a kashe su in an kama gari da yaki, amma sai suka jingina wa Musa (A.S) karyar cewa ya kashe mata da dukkan yara da duk wata mata da namiji ya taba kusantar ta a lokacin da ya ci nasara a kan wani gari domin su cimma burinsu irin wannan a kan mace. Game da gado kuwa matukar uba yana da da namiji to mace ba ta da komai, amma duk da irin wadannan dokokin ba mu ganin ana sukan wannan addini a matsayin wani Addini da ya tauye hakkin mace. Hada da cewa a bisa dokarsu adadin matan da za a iya aura ba kayyadadde ba ne, amma ba mu ga mai suka ba a A kissoshin Annabawa da suke cikin Attaurar ya zo game Annabi Sulaiman (A.S) yana da mata dari bakwai da kuyangi dari uku, Dawud (A.S) yana da mata biyu, haka ma Ibrahim (A.S). Kuma matar Musa (A.S) Maryam ta yi wa Haruna (A.S) magana don Annabi Musa (A.S) ya yi mata kishiya bakar fata ‘yar Habasha kamar yadda ya zo a Littattafansu[21]. A nan ya kamata mutane su yi hukunci tsakanin irin wadannan dokoki da na musulunci, su kuma kwatanta su su ga ni’imar da Allah ya tanada a cikin addininsa na musulunci da kuma kamalarsa, da kula da hakkin mata da maza da ba a taba samunsa ba a cikin wani Addini a tarihin rayuwar dan Adam[22]. Mace A Cikin Kiristanci
Babu wani bambanci sosai a mafi yawan dokoki tsakanin Kiristanci da Yahudanci, misali game da hukuncin lullubi da hijabi wanda akwai shi a Yahudanci da Kiristanci amma sai suka sassauta hukuncinsa, wanda a farkon Kiristanci rashin sanya shi laifi ne kuma aibi ne mai girma da saba doka. Duba ka ga abin da ya zo a Risalar Bulus zuwa ga mutanen Korentis da umarnin a aske gashin duk wata mata da ba ta da hijabi (lullubi) don ta ladabtu[23]. Hakan nan suka sassauta shi saboda faruwar juyin juya halin masana’antu a kasashen turai da sunan saukaka aiki ga mace don ta ji dadin yin aiki a gona da ma’aikatu, sai abin ya yi yawa har coci ta yi muwafaka da shi. Game da auren mace sama da daya kuwa, wasu sun kayyade shi da hudu, wasu kuma ba iyaka, kamar yadda yake gun Yahudawa, amma sai ga shi an soke musu wannan hukunci duk da kuwa ya saba da kissoshin yawan matan Annabawa (A.S) da suke kawo wa a cikin Injila. Abin takaicin shi ne; ba mu san dalilin sukan auren mace fiye da daya zuwa hudu da wasunsu a yammacin duniya suke jifan musulunci da shi ba alhalin suna da sama da hakan a littattafansu.
|