Tarihin Mace A Al'aduIrin wadannan misalai suna da yawa a kowane bangare na rayuwar musulmi da ya hada da cinikayya, da zamantakewar al’umma, da ibada, da tattalin arziki, da siyasa. Yawancin irin wannan a kasashen musulmi yana tasowa ne daga rashin sanin musulunci da hukunce-hukuncensa ko kuma cakuda shi da al’adu, shi ya sa ma ba ya shafar mace kawai har ma da namiji. Al’ummarmu tana da bukatar ta mike ta san hukuncin addini kamar yadda Allah ya aiko Manzo (S.A.W) da shi, wannan kuwa yana bukatar jan aiki a kan malamai kuma da ita al’ummar. Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai Masdarorin Madogarar Wannan Littafin:
Kur’ani mai girma Tafsirul mizan, Allama diba’diba’i Risalar Bulus: zuwa ga mutanen Korentis Hukukul insan fil islam Al’mar’atul jadida Jaridar Al’ahram: bugu: 28/6/1964 Shara’i’ul Islam, muhakkikul hilli Minhajus salihin, sayyid khu’I
|