Tarihin Mace A Al'aduFarisawa Da Larabawa Da Yunan
Amma Yunan da Yankin Larabawa da Tsohuwar Iran a wajansu gida da maza ne ake lissafinsa ba da mata ba, har ma kusancin da a kansa ake gado[12] da maza ne ake la’akari ba mata ba, babu kusancin da ya shafi mace da ake kiyaye shi, kamar na uwa, ko ‘ya, ko ‘yar’uwa, kusancin mace da ake kiyaye wa kusanci ne na dabi’ar jinsi [saduwa] da haihuwa, da auratayya. Mace A Gun Larabawa
A al’adun Larabawa idan ‘ya tana gidan uba ko miji suna iya yin duk abin da suka ga dama da ita, kimar mace hatta ta ranta ba ta da wani alfarma, duba mana ka gani farkon shahidi a Musulunci mace ce. Dukiyarta ta namiji ce koda kuwa sadakinta ne, kuma koda kuwa kasuwanci ta yi, balle gado da haramun ne a gare ta, uba ko dan’uwa shi ne zai aurar da ita ko ta ki ko ta so, wannan al’adun na Jahiliyyar larabawa da akwai tsammanin cewa irin su ne suka shiga wasu yankunanmu da sunan Musulunci. Jaririya kuwa ko yarinya ba ta tsira daga binnewa da ranta ba, suna ganin halittar mace aibi ne, da musifa, da bala’i garesu[13], musamman ma idan an ribace ta a yaki, a wajansu wannan wani aibi ne da babu kamarsa, don haka a binne ta ma da rai don kada ta taso ta zama aibi ga al’ummarsu. An ce farkon wadanda suka binne ‘ya mace su ne Bani tamim sannan sauran larabawa suka dauka, wannan ya kasance ne sakamakon ribace su da sarki Annu’uman dan Munzir ya yi ne[14], sai wannan abu ya fusata su suka fara binne na raye da ransu, haka nan idan aka yi wa wani albishir[15] da ‘ya mace sai ka ga yana buya daga mutane don kunya na abin aibi da ya samu, amma idan namiji ne yana mai farin ciki komai yawansu, wannan ma ba ya isar sa har sai ya yi da’awar dan zina ma cewa nasa ne, har ma ya kan iya kai wa ga yaki ko fada a kan ‘ya’yan zina[16]. Amma wasu lokuta wasu gidaje sukan ba wa mace dama ta auri wanda take so, ko yaya dai, mu’amalarsu da mata mu’amala ce da ta cakuda da ta al’adun daulolin da suke kewaye da kasashen larabawa kamar Iran da Rum. A yankin Larabawa mace wata kalma ce ta wula- kanci a gaya wa namiji ita, kuma kalma ce ta kaskanci, haka nan mace a wasu al’ummu ta zama murhu ne kawai na dafa abinci ko wanke kaya da yara, sai kuma idan bukatar namiji ta taso, amma duk abin da ya shafi ci gaban al’umma wannan wani abin mamaki ne a ga mace a ciki. Duba ka ga wurare kamar kasashanmu kusan ala’amarin mace yana da ban takaici ta yadda a komai kana iya ganinta idan ya shafi gida kawai, amma wani abu ko da kuwa na Addini ne da ya shafi al’umma gaba daya ne to a nan wani abin mamaki ne a ganta a ciki, ba ta isa ta ziyarci makabarta ko masallaci ba, ba a ma tunanin wurin mata. Haka ma shugabantar wata kungiya ko kafa wani abu na shugabantar wasu jama’a, sabanin wasu kasashe kamar Farisa da aka samu ci gaba ta wannan bangare da mace tana iya yin ilimi mai zurfi har ta kai matsayin mai iya yin ijtihadi a hukunce-hukuncen Addini, a yau a cibiyoyin ilimi mata sun riga sun mamaye ko’ina har sun wuce maza a fagage da dama. Mace A Gun Yunan (Girika)[17]
Amma a Yunan[18] al’amarin mata ba shi da bambanci da na Rumawa suna la’akari da namiji ne a dokokin zamantakewa, komai na namiji ne ba abin da mace take da shi, amma a bangaren laifi ana hukunta ta, haka ma in ta jawo wani abu na amfani to wannan na namiji ne, suna ganin mace kamar kwayoyin cuta ne masu cutar da al’umma, amma ta wani bangare abu ce ta amfanin al’umma, kuma idan ta sake ta yi laifi ko yaya yake, to ta shiga uku. Suna ganin mace kamar wani ribataccen yaki ne da yake kurkuku wanda idan ta kyautata amfani ba nata ba ne, idan kuwa ta munana ta dandani kudarta, kuma ba a gode mata, suna ganin tunaninta sharrin ne kawai, saboda haka ba ta isa a bar ta a
|