Tafarki Zuwa Gadir Khum



Sai ya ce, “sako mafi nauyi littafin Allah, gefensa a hannun Allah, gefe a hannunku, dayan karamin shi ne zuriyata. Hakika Ubangiji Mai tausayi, Masani, ya ba ni labari cewa su ba zasu taba rabuwa ba har abada har sai sun riske ni a tafki. Sai na roka musu wannan a wajen Ubangijina. To kada ku shiga gabansu, sai ku halaka, kada ku tsaya can bayansu, sai ku halaka”.

Sannan ya riki hannun Ali (A.S) har sai da aka hango farin hammatarsa, mutane suka gan shi gaba daya, sannan ya ce: “Ya ku mutane, wanene ya fi wa muminai kawukansu?”.

Suka ce: “Allah da Manzonsa sune mafi sani”.

Sai ya ce: “Hakika Allah Shugabana ne, ni kuma Shugaban mutane. Kuma ni ne na fi wa muminai kawukansu. To duk wanda nake Shugabansa, wannan Ali Shugabansa ne!”. ya maimaita sau uku, a ruwayar Ahmad ya maimaita sau hudu.

Sannan ya ce: “Ka jibanci lamarin wanda ya mika masa wuya, ka ki wanda ya ki shi, ka so wanda ya so shi, ka taimaki wanda ya taimake shi, ka tabar da wanda ya ki taimakon sa, ka juya gaskiya tare da shi duk inda ya juya. Ku saurara! Wanda yake nan ya isar wa wanda ba ya nan”.

A wannan lokaci mawakin Manzon Allah, Hasan bn Sabit ya shiga waka don ya koda wannan al’amari da ya zama idi ga musulmi. Yana cewa:

Annabinsu yana kiran su a ranar Gadir

A Khum an ji Annabi yana mai kira

Yana cewa wanene Shugabanku Mahaliccinku

Suka ce ba tare da musun da ya bayyana ba



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 next