Tafarki Zuwa Gadir Khum



Isar Da Sako Bayyananne

Kwanakin hajji mafi girma sun wuce, yanzu lokaci ya yi tawagar mahajjata su koma gidajensu, mutanen Makka suka zama suna kallon jama’a mai yawa cike da mamaki. Ga su suna barin kasa mai tsarki inda Jibril ya sauka yana dauke da sakon karshe na sama. Manzo (S.A.W) ya bar Makka ransa cike da natsuwa da yaduwar musuluncin da ya zama addinni farko a lokaci kankani a yanki mai fadi na duniya.

Runduna ta isa yankin Juhufa a mararrabar hanya. Rana ta take a sama, zafinta ya bugi sahara, ga rayirayi ya dauki zafi. A wannan wuri mai zafi na duniyar Allah, Jibril (A.S) ya sauka da sakon karshe. “Ya kai wannan Manzo! ka isar da sakon da aka saukar maka daga Ubangijinka, idan ba ka yi ba, to ba ka isar da sakon sa ba, kuma Allah ne yake kare ka daga mutane”.

Yana bayyana daga maganar nan ta Kur’ani, wacce ta dauki matakin gargadi cewa, lallai akwai wani babban al’amari da ya wajaba a kan Annabi (S.A.W) ya isar da shi zuwa ga al’ummar da aka fare ta kafin wasu ’yan shekaru. Sai kawai aka yi wa tawagar alhazai mufaja’a da kiran Annabi da cewa a tsaya a sararin nan mai tsandauri, mai wahala da zafi, babu wata bishiya da matafiyi zai sha inuwa, babu ruwa da mai kishi zai kashe kishinsa, aka sanya alamar tambaya da mamakin al’amarin Annabta!.

Mutum ba zai iya kore abin da  Manzo ( S.A.W) yake ji ba na makomar musulunci bayan wafatinsa, musamman da ya zama yana ganin karshen rayuwarsa ya zo, ba abin da ya rage masa a duniya sai wani dan taki. Musulmi suka rika tsinkayo zuwa ga Annabi (S.A.W) yana hawa tuddai da wasu sahabbansa suka jera, ya tsaya a kai yana mai kallo zuwa ga gomomin dubunnai na wadanda suka yi imani da ya shi, suka karbi sakonsa, idanunsa suna yawo da tunanin al’amari mai zuwa da ba wanda ya san sirrinsu sai Allah. Ga jawabin da Manzo (S.A.W) ya yi:

“Lallai an kira ni na amsa, kuma ni mai barin nauyayan alkawura biyu a gare ku ne: Littafin Allah da Ahlin gidana. Ku duba ku gani me za ku yi bayana (game da al’amarinsu) domin su ba za su rabu ba har sai sun riske ni a tafki”. Ali dan Abi Dalib (A.S) ya kasance yana kusa da shi, sai ya kira shi ya yi riko da hannunsa ya gabatar da shi ga duniya gaba daya. “Shin ba nine waliyyin muminai ga kawunansu ba, kuma matana iyayensu ba?” Sai ga amsa da murya mai karfi ta ko’ina.

“Haka ne ya Manzon Allah!”.

Sai Annabi (S.A.W) ya daga murya, yana mai daga hannun Ali “Duk wanda nake Shugabansa, to wannan Ali Shugabansa ne. Ya Ubangiji (S.W.T) ka taimaki wanda ya bi shi, ka kuma ki wanda ya ki shi”, Manzo ya isar da sakonsa. Sai Jibril (A.S) ya sauka yana mai shelanta bishara daga sama: “A yau ne na kammala muku addininku, na cika ni’imata a gare ku, kuma na yardar muku da Musulunci shi ne addini”. Sai farin ciki ya yadu a wannan sahara mai tsananin zafi. Hasan dan Sabit ya mike don farin ciki, yana mai nanata wadannan baitoci, yana mai godiya da yabo:

Annabinsu (S.A.W) yana kiran su ranar Gadir a Khum

Ya mamakin jin Annabi! yana mai shelantawa



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 next