Tafarki Zuwa Gadir KhumFararrun Abubuwa A Hanyar Hajjin Karshe Al’amari Na Farko A watan Zul ka’ada, a shekara ta goma hijira, Annabi (S.A.W) ya shelanta niyyar zuwa hajjin dakin Allah (S.W.T). Ashirin da biyar ga wannan wata karaukoki suka nufi Makka (Wajen son kowa), Ya yi sa’ayi tsakanin duwatsun biyu a motsi da yake tunatarwa game da babar Isma’il (A.S) yayin da take binciken digon ruwan sha ga danta Isma’il (A.S), ya hau dutsen Safa ya kalli Ka’aba mai girma, ya shelanta karewar bautar gunki. “Ba abin bauta sai Allah daya, Ba shi da abokin tarayya, Mulki da godiya sun tabbata a gare shi. Shi mai iko ne a A Arfa Annabi (S.A.W) ya tsaya yana mai huduba, ya yada al’adun Musulunci tsakanin musulmi, yana mai albishir da bankwana na aminci. Sannan ya shelantar da wurgi da kabilanci da kuma wajabta girmama mutum: “Ya ku mutane! hakika Ubangijinku daya yake, kuma babanku daya ne, dukkanku daga Adam (A.S) kuke, shi kuwa Adam daga kasa yake, Kuma mafi girmanku a wajen Allah (S.W.T) shi ne mafi tsoron ku ga Allah, balarabe ba shi da wani fifiko a kan ba’ajame sai da takawaâ€. Sannan ya wuce yana mai kafa sababbin dokoki da aminci da soyayya da kaunar juna zai zama a cikinsa. Ya ce: “Duk wanda yake da amana, to ya ba da ita zuwa ga wanda ya ba shi amana. Kuma ribar jahiliyya babu shi, kuma farkon riba da zan fara saryar da shi shi ne ribar Ammina Abbas dan Abdulmudallib, Annabi bai manta bayanin hakika mai girma ba ta hanyar da zasu bi bayansa (S.A.W). Ya ce “Ya ku mutane! Lallai muminai ’yan uwa ne, dukiyar dan’uwa musulmi ba ta halatta gun dan’uwansa musulmi sai da yardarsa. Kada ku koma kafirai bayana sashenku yana dukan (saran) wuyan sashe. Kuma hakika ni na bar muku abin da idan kun yi riko da shi ba za ku taba bata ba bayana har abada - littafin Allah da Ahlin gidanaâ€.
|