ZamaninJuyin Juya Hali



Mufaddil ya ce: Ya shugabana (imam Sadik) me zai yi da mutanen Makka? Sai ya ce: Zai kira su cikin hikima da wa’azi kyakkyawa, sai su bi shi, sai ya sanya musu wani mutum daga ahlin gidansa, sannan sai ya fita ya nufi Madina[21]. Da wannan ne muke iya cewa kiransa da farko zai kasance na wayarwa da ilmantarwa ne ba na yaki ba.

 Amma bayan ya tafi Madina sai mutane Makka su kashe halifansa, sai ya sake dawowa Makka sai su tuba sai ya karbi tubansu, ya sake sanya musu wani halifan ba tare da ya yake su ba: “Sai ya yi musu wa’azi ya yi musu gargadi ya sanya musu wani halifan daga cikinsu”[22].

Amma bayan imam (A.S) ya kama hanya zuwa Madina sai mutanen Makka su sake kashe halifansa na biyun da ya sanya musu, a nan ne ake cewa sai ya dawo zuwa Makka da karfin soja domin daukar fansa a kansu, ya gaya wa sahabbansa: “Ku koma kada ku bar wani daga cikinsu sai wanda ya yi imani”[23].

B- Dubarun Matakin Soja

Wata hanyar da imam Mahadi (A.S) zai yi amfani da ita, ita ce hanyar karfin soja, imam ba ya amfini da karfin soja wajan da yake bukatar sulhu da aminci, sai dai abin da ba mu da masaniya a kai shi ne yaya karfinsa na tsaro yake, kuma da wadanne dubaru ne zai yi aiki, sai dai akwai magana gamammiya game da tsarin tsaronsa da karfin soja da suka zo a ruwayoyi kamar haka:

1- Kashe makiya Allah;

2- Tsarkake duniya daga shirka da munafunci;

3- Tsarkake kasa daga dukkan zalunci da danniya;

4- Take duk wani azzalumin sarki da shugaba;

5- Yaki a kan tawilin kur’ani kamar yadda Annabi ya yi yaki a kan saukarsa[24].

A bisa asasin abin da ya zo a ruwayoyi: farkon yakin da imam Mahadi (A.S) zai yi zai kasance da Sufyani ne. Kokarin da Sufyani zai yi na kashe imam (A.S) shi ne farkon abin da zai sanya imam (A.S) ya gan shi a matsayin mai tawaye ga daularsa[25]. A wannan yakin za a kashe Sufyani kuma mulkin imam Mahadi (A.S) zai tabbata a dukkan yankunan da Sufyani yake mulki wato Iraki da Siriya[26].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next