ZamaninJuyin Juya Hali



Amma batun cewa ya zo da addini sabo kamar yadda ya zo daga maganganun wasu mutane ba shi da inganci[46].

Haka nan tunanin cewa zai zo da wani kur’ani daban ba wannan ba wannan ma batacce ne, domin Mahadi mai imani ne da littafin Manzo da sunnarsa, kuma babu wata mazhaba da take da kokwanto a kan hakan[47]. Imam Ali yana cewa: Sai ya nuna muku yanda hanyar adalci take, ya raya matacce daga Kur’ani da Sunna[48].

Ba komai raya matacce yake nufi ba sai gyara tafsirin barna da karkata da ake yi wa littafin Allah da fitar da ma’ana da tawilinsa na gaskiya, da fitar da badininsa na ainihi, kuma wannan yana nufin hukumar Allah a bayan kasa da gudanar da adalci a dukkan duniya.

 

Na shida- ma’abota juyin imam Mahadi (A.S)

Samuwar mutane na gari masu sadaukarwa ga kowace fikira abu ne na dole domin cin nasararta, don haka juyin duniya dole ne ya kasance yana kunshe da tunanin samuwar mabiya daga kowane yanki na duniya da bai kebanta da wata kasa ba.

Saboda muhimmancin wannan juyin na Mahadi (A.S) dole ne ya kasance bai takaita da shi ba, don haka ne ya shagaltu da tarbiyyar mutane na gari wadanda zasu kutsa wa wannan jarrabawa mai tsanani, kuma hadisai masu yawa sun zo game da mataimakansa wadanda suke nuna farkon mataimakansa da mutane 313 ne[49].

Sahabbansa zasu kasnce daga kasashe daban-daban wadanda yawancinsu daga gabas ta tsakiya ne kamar Misra, Iraki, Labanon, Siriya, Urdun, Falasdin, Jariral larabawa, Makka, Madina, Iran, Afganistan, Fakistan da sauran kasashen gabas ta tsakiya da …

A bisa wannan asasin ne za a iya cewa: mafi yawan rundunar imam Mahadi (A.S) tana gabas ta tsakiya ne, sannan daga baya yankunan Afrika da Kabrus da Yaman da Turai da gabas mai nisa su kawo dauki ga rundunarsa don bayar da gudummuwa ga wannan juyin duniya mai girma[50].

 A wasu ruwayoyi mabanbanta an ambaci wasu daga garuruwan mataimakansa kamar: Dalikan, Amman, Askar Makram, Basar, Siraf, Shiraz, Isfahan, Karaj, Kum, Kazwin, Armeniya, Zaura’, Abadan, Musil, Nasibiyin, Balis, Halab, Hims, Damashk, Baitul Mukaddas, Gazza, Fusdad, Askandariyya, Al’afranj, Urdun (Jodan), Madina, Makka, Da’ifa, Marwa, Hijir, Arafat, Ramla, Akka, Andakiya, Yamama. An kuma ambaci yawan mutanen wasu garuruwa a ciki kamar Dalikan da take da mataimaka 24 ne, kamar yadda aka ambaci mataimaka da sunan taskoki da ba na zinariya ko azurfa ba[51].

Ruwayoyi masu yawa sun zo suna yabon mataimaka wannan jagoran na juyin duniya mai girma “Imam Mahadi” (A.S) kamar haka:

-Mazaje ne muminai da suka san Allah hakikanin saninsa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next