ZamaninJuyin Juya HaliDa farko Sufyani wanda yake daga alayen Abu sufyan zai zo Kufa wajan imam (A.S) da sunan sulhu, kuma mutanen Najaf da Kufa zasu karbi jagorancin imam Mahadi (A.S) su nemi tsayar da sallar jumma’a a bayansa, al’amarin da zai tunatar da su sallar Annabi (S.A.W), daga nan ne motsin juyi da neman ‘yanci zai fara, juyi ya rika daduwa a kowace rana[17]. Na Hudu- Dubarun Juyin Imam Mahadi Na Duniya Saudayawa yakan zo a kwakwalen mutane cewa juyin imam Mahadi juyi ne na jagorancin soja da yaki, amma idan muka duba dubaru da salon da yake dauka kamar yadda ya zo a ruwayoyi zamu ga salon dubaru na wayarwa da al’adu shi ne gaba. Don haka ne dubaru da salon da zai dauka suna iya kasuwa gida biyu: A- Dubarun wayarwa da al’adu
Babban hadafi a wannan fage shi ne: yada addinin musulunci a gaba dayan duniya da raya kur’ani da sunnar Allah da dawo da mutane a kan tafarkinsu[18]. Imam Ali yana kawo wannan al’amari a huduba ta 182 ta Nahajul balaga game da imam Mahadi (A.S) yana mai fadin dubarunsa na wayar da mutane: “Hakika ya sanya wa hikima tufafinta… ragowa ne daga ragowar hujjarsa, halifa ne shi daga halifofin annabawansa…â€[19]. Jumlar da take cewa ya sanya tufafin hikima yana nuni zuwa ga farkon juyinsa ne yayin da, da farko ya fara da bayyana da fuskar mai hikima mai ilimi. A bisa hikima ce wacce a cikin kur’ani aka kirata da alheri mai yawa zai fara juyin ilimi, da wannan ne zai fara yin galaba a kan dukkan addinai da masu da’awowin (kiraye-kirayen) karya. Haka nan a huduba ta 138 ya zo cewa: Yana sanya burace-burace su kasance masu bin shiriyar wahayi… yana raya mataccen littafin da sunna[20]. A wannan huduba ya nuna cewa imam Mahadi zai zabi hanyar juyi ta hanyar kyawawan dabi’un domin samar da juyin kyawawan halaye a cikin kawukan mutane, ta yadda zai mayar da son ransu ya zama bin shiriyar Allah, sannan kuma zai nuna fassara da tawili sahihi game da kur’ani da sunnar Annabi (S.A.W), kuma ya dawo da koyarwar kur’ani da sunna da aka manta da ita aka gafala gabarinta aka kashe ta. Wani dalilin game da cewa zai fara yin aikin wayarwa da ilmantarwa ne kafin yaki shi ne:
|