MATSAYIN IMAM SAJJAD(A.S).



  Nassoshin tarihi da riwayoyin hadisi wadanda suke hannunmu basu faiyace samuwar wata matsananciyar harakar fama a siyasance wacce Imam yake aiwatarwa ba. Wannan rashin bayyanannar fama yana da dalilai, kamar su wanzuwar wani yanayi na jabberanci da azabtarwa mai mamaye da rayuwar al’umma, abin da ya tisalta wa mabiyan Imam wadanda su kadai ne masu masaniya  kan rayuwarsa ta fuskar siyasa da su yi riko da takkiya. Sai dai martani matsananci wanda magabta (hukuma) suke mayarwa  yana nuni da aikin jihadi mai zurfin tasiri da ake yi. Yayin da karfin mulki iri na Abdulmalik Ibn Marwan,wanda ake daukarsa  a matsayin mafi karfin sarakunan Umayyawa, yayin da yake daukar mafi tsanani da tsaurin mataki kan Imam Bakir, ba wata tantama, wannan yana nuna cewa halifan yana jin tsoron hadarin da harakar da Imam da mabiyansa ke gudanarwa take tattare da shi ne. Da a ce Imam ya shagaltu ne da aiyukan ilmantarwa kadai ba tare da ya ba da himma kan gina tunani da tsare-tsare ba, to da sai mu ce ba  maslaha ce ga masu mulki ba su matsawa Imam din lamba domin wannan mataki yana iya sa wa shi da mabiyansa su dauki matsayin fushi matsananci tamkar wanda mai tawayen nan ba’alawe Shahidin Fakh, watau Hussain bin Ali ya dauka.

A takaice, ana iya fahimtar matsanancin matsayin da hukuma ta dauka dangane da Imam Bakir (a.s) ta fuskar mayar da martanin da take yi kan aiyukan Imam masu sabawa da ra’ayin masu iko.

Daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a karshen  rayuwar Imam Bakir (a.s) akwai kiransa da aka yi zuwa hedkwatar halifancin Umayyawa watau Sham (Dimashka). Halifofin Umayyawa sun  yi niyyar bincikar matsayin  Imam kan hukuma. Wannan ya sa suka yi umurni da kama shi da kuma kai shi Sham cikin cikakken tsaro. A wasu riwayoyi an ce wannan umurni ya hada har da dansa matashi watau Ja’far Sadik.

An kawo Imam fadar halifa. Kafin haka Hisham ya yi wa jama’arsa shiftar yanda za su fuskanci Imam yayin da yake shiga. Abin da ya shirya shi ne, shi halifa zai fara bijiro da tuhumce-tuhumce kan Imam sannan jama’a su ci gaba.

 Abubuwa biyu yake da niyyar cimmawa: na farko shi ne raunana azamar Imam da sanya masa rashin yarda da kai. Na biyu: Kokarin sukar Imam a cikin taron da ya hada jagaban jama’ar halifanci da kuma na Imamanci a waje guda, sannan daga bisani a yada wannan cin zarfin ta hanyar kakakin fada kamar masu jawabi da masu wa’azin sarki da kuma ‘yan laken asiri, kuma da haka ne Hisham yake fatar samawa kansa nasara kan abokin hamayyarsa.

Da Imam ya shigo fadar halifa, sabanin yanda masu shigowa suka saba da yin gaisuwa ga halifa da sunan shugaban muminai, sai ya fuskanci dukkan mahalarta yana mai nuni ga ilahirinsu, ya ce: assalamu alaikum. Sannan ba tare da jiran izinin zama  ba sai ya yi zamansa.

Wannan abin da Imam ya aikata ya cinna wutar  hasada da kufe  a zuciyar Hisham. Nan take sai ya fara jefa muggan maganganu yana cewa: ‘ Ya Muhammad Ibn Ali ba’a gushe ba wani daga cikinku yana rarraba kan musulmi, yana kiran mutane da su bi shi, yana kuma da’awar shi ne Imami (shugaba ) saboda wauta da karancin sani ………[12]Ya dai ci gaba da sukar sa.

Bayan Hisham ya gama sai jama’a suka karba, suka ci gaba da maimata wadannan tuhumce-tuhumce da soke-soke. A tsawon wannan lokaci Imam uffan bai ce ba, yana sunkuye da kai cikin natsuwa, yana jiran damar ba da amsa.  Yayin da mutanen nan suka kare duk abin da ke gare su, wuri ya yi  tsit, sai Imam ya mike ya fuskanci jama’a, ya yi yabo ga Ubangiji ya yi salati ga Manzonsa (s.a.w.a) kana ya yi jawabi.

Wannan jawabin ya kunshi kalmomi ne matakaita masu kwankwasa tare da bayyana rauni da kuma sakar akala tamkar kumaki wanda wadancan ‘yan amshin Shatan suka yi. Kazalika ya nuna matsayi da daukaka da Ahlulbaiti suke da shi, kamar yanda ma’aunan musulunci suka tabbatar, ya kuma wulakanta duk abin da halifa da jama’arsa suka mallaka na kazamar dukiya da kuma iko. Ya ce:- ‘Ya ku mutane ina kuke tafe ne? Ina aka nufa da ku? Da mu Allah ya shiryi na farkonku kuma da mu ne zai cikata (shiryar da) na karshenku. Idan abin gaggautawa na mulki naku ne to (ku sani cewa ) abin da aka jinkirtar  na mulki namu ne sannan kuma babu wani mulki bayan namu saboda mu ne ma’abota kyankkyawan karshe. Allah mai girma da daukaka yana cewa: “Kuma kyakkyawan karshe ya tabbata ga masu takawa”[13].

Wadannan kalmomi matakaita wadanda suka kunshi wawaitarwa da kokowa da zalunci, da albishiri da bazarana, da tabbatarwa da kuma raddi duk a lokaci guda, ba shakka masu girgizawa ne tare  da sa mai sauraro yin imani da cewa mai fadarsu shi ne ma’abocin hakki. Sakamakon haka, Hisham sai ya ga babu abin da zai yi face umarni da a jefa Imam kurkuku. Imam Bakir ( a.s ) ya ci gaba da aikinsa na gyara hatta a cikin gidan kaso, al’amarin da ya yi tasiri matuka kan fursunoni. Da labari ya kai ga Hisham,sai ya ji tsoron cewa irin wannan farkawa za ta faru a hedkwatarsa wacce aka kiyaye daga tasirin Alawiyyawa. Sai ya yi umarni da fitar da  wannan fursunan (Imam Bakir) tare da wadanda suka dauki ra’ayinsa da kuma aika su da daggawa zuwa Madina wanda shi ne mazaunninsa. Umarnin ya hada da cewa idan sun kama hanya kada kowa ya yi wata hulda da wannan ayari wanda halifa yake fushi da shi.  Kada a ba su guzurin abinci ko ruwan sha.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 next