MATSAYIN IMAM SAJJAD(A.S).Saboda haka takardar Imam tana bayyana matsayinsa kan yanayin zamaninsa ne. Nassin wannan wasika yana nan cikin littafin Tuhaful Ukul.[2] Akwai kuma wasikar da Imam ya aikewa Abdulmalik ibn Marwan a matsayin jawabi kan wata wasikarsa wacce take dauke da aibantawa ga Imam saboda ya auri wata baiwar da ya yanta. Abin da Abdulmalik yake son baiyanawa Imam (a.s.) shi ne yana sane da duk abin da yake aikatarwa hatta al’amuran da suka kebance shi. Kazalika yana nufin tunatar da Imam (a.s) da dangantakarsa da shi da zimmar jan hankalinsa. A jawabin da ya rubuta, Imam ya baiyana ra’ayin musulunci a kan wannan mas’ala yana mai takidin cewa fifikon imani da musulunci ya kore kowani fifiko. Sannan ta hanyar kinaya, mai gwanin kyau, imam yayi ishara da hali rin na jahiliyya wanda iyayen halifa suka rayu a kai, la’alla ya hada har da rayuwar halifan shi kan shi. Ya ce: “ Babu karanta ga musulmi, karantar jahiliyya ce kawai karantaâ€. Da halifa ya karanta kalmomin Imam (a.s) ya fahimci ma’narsu,cikakkiyar famta,kamar yanda dansa Sulaiman ya tsinkayi ma’anar yayin da ya ce da mahaifinsa: “Ya Shugaban Muminai alfaharin da Ali bn Hussaini ya yi hakika ya yi tsanani!†Saboda gogewarsa ta siyasa,halifa sai ya amsa wa dansa da abin da zai nuna masa cewa ya fi shi sanin abin da karo da imamin shi’a zai hafar. Ya ce da shi: “Da na kada ka fadi haka,domin wadannan harsunan Bani Hashim ne masu tsaga dutse, masu kamfata daga teku. Da ma ai Ali ibn Hussaini yana bayyana daukakarsa a yanayin da sauran mutane suke fankamar mika wuya.†Wani misali mai nuna matsayin da Imam ya dauka shi ne yin watsi da wata bukatar Abdulmalik bin Marwan. Abdulmalik ya sami labarin cewa akwai takwabin Manzon Allah (s.a.w.a) wurin Imam sai ya aiko yana neman ya ba shi kyautarsa ya kuma yi barazanar yanke abin da ake baiwa Imam daga baitul mali.Sai Imam (a.s) ya rubuto masa:- ((Bayan haka, Lallai Allah ya lamunce wa masu tsoronsa mafita ta inda suke ki, da arziki ta inda basu tsammani. Mai girman ambato ya ce (Lallai Allah ba ya son duk wani mai tsananin ha’inci mai yawan kafirci), sai ka duba ka gani wane ne daga cikinmu ya dace da wannan aya?[3])) A wasu wurare muna ganin Imam Sajjad (a.s) yana motsawa cikin natsuwa da kuma garkuwa da tarbiyar dai-daiku da gina mutumtaka ta musulunci bisa karantarwar mazhabin Ahlulbaiti da yaki da baude-baude da sauransu. Da wannan aikin ne bisa hakika, ya dauki matakin asasi na farko a kan tafarkin tabbatar da manufar mazhabin Ahlulbaiti wanda ita ce kafa jama’ar musulunci karkashin inuwar salihar hukumar musulunci bisa misalin hukumar Manzon Allah (s.a.w.a) da Ali bin Abi Talib (a.s). Kuma kamar yanda muka ambata Imam (a.s) da mabiyansa basu nemi daidaitawa da hukuma mai kamu da azabtarwa ba duk da cewa sun bi hanyar da a zahiri tana daidaitawa da hukuma. Daga cikin mabiyansa akwai wadanda aka kashe ta kazamar hanya, wasu an daure wasu kuwa an kore su nesa da mutanensu da gidajensu. Imam da kansa a kalla sau daya an tusa keyarsa a cikin kangi a cikin halin torartawa da wahala daga Madina zuwa Sham, sau da yawa kuma ya fada cikin nau ‘o’ in cutarwa da azabatarwa. Daga karshe halifan banu Umayya, Walid bin Abdulmalik ya ciyar da shi guba. Imam (a.s) ya yi shahada a shekara ta 95 bayan hijira. RAYUWAR IMAM BAKIR (A.S)
|