MATSAYIN IMAM SAJJAD(A.S).



Akwai hujjoji a hannunmu wadanda suke bayyana wannan alaka mai ba wa mabiya manufofi da karantarwa mabayyana da kuma tsara al’amuransu bisa tafarki hadadde, lasaftacce.

Misali; A farkon haduwar Jabir Alju’fi da Imam Bakir(a.s) sai ya masa wasiyya da kada ya fada wa kowa cewa daga Kufa yake ya kuma  yi fita irin  ta mutanen Madina .Da wannan Imam yake koyar  da darasin rike sirri ga wannan  sabon dalibi  wanda ya ga alamun  iya rike sirri tattare da shi. Wannan dalibi mai cancanta sai ya zama ma’abocin sirrin Imam.

  Tsakaninsa da hukuma kuwa lamarin ya kai ga abin da Nu’man bin Bashir ya ce:-

“Ina mai lizimtar Jabir bin Yazid Alju’fi yayin da muke Madina sai ya shiga wurin Abu’far (a.s) ya yi masa bankwana ya fito yana farin ciki. (Muka kama hanya) har muka isa Al’ukairaja, daga kewayen Madina, a ranar Juma’a. Muka yi salla. Mun kama tafiya kenan sai ga wani mutum dogo mai duhun fatar jiki da wasika a hannunsa. Sai Jabir ya karbe ta ya sunbace ta yasanya ta kan idanunsa. Sai ga shi a rubuce(( Daga Muhammad bin Ali ( Bakir) zuwa ga Jabir bin Yazid)), ga kuma danyen bakin yumbu a kanta. Sai ya ce da shi: ‘Yaushe rabonka da shugabana?’ Sai mutumin ya ce: ‘Dazun nan; sai ya ce: ‘kafin salla, ko bayan salla? Sai ya ce : ‘Bayan salla.’ Sai ya warware hatimin ya ci gaba da karantawa, yana daure fuska har ya kai karshenta, sannan ya nade ta. Daga nan ban sake ganinsa yana dariya ko farin ciki ba har muka isa Kufa”.

Numan ya ci gaba da cewa: “Mun isa kufa cikin dare, kashegari sai na tafi wajen Jabir Alju’fi saboda girmama shi, sai gashi ya fito bisa dokin kara yana rataye da wadansu kulle-kulle, tamkar yanda mahaukata ke yi, yana rerawa kamar haka:

‘Na san Mansur mutumin mutane;

Mai umurni ba’a umurtansa’

da wasu baitoci irin wannan. Sai ya kalli fuskata na kalli tasa amma bai ce da ni komai ba, ni ma ban ce masa komai ba. Sai na juya ina kuka saboda abin da na gani. Sai jama’a, babba da yaro, suka kewaye mu. Sai ya  tafo har ya shigo dandali, ya kama zagawa tare da yara mutane na cewa Jabir bin Yazid ya haukace. Wallahi bayan ‘yan kwanaki sai ga takardar Hisham Ibn Abdulmalik an aiko ta gare ni kan batun shi. Tana cewa: ‘Ka binciki wani mutun mai suna Ja’bir Ibn Yazid Alju’fi ?’sai mutane suka ce: ‘Allah ya kiyaye ka’. Da mutun  ne mai ilmi da daraja da sanin hadisi, ya yi aikin haji sai ya haukace. Shi ne wancan a dandali bisa dokin kara yana wasa da yara. Sai na ce: “Godiya  ta tabbatar ga Allah wanda ya hutar da ni kisansa’.[10]

  Wannan misali ne na alaka tsakanin Imam da mabiyansa na kusa. Yana bayyana tsananin  tsari sa alaka  kazalika yana nuna wani misali na matsayin hukuma kan mabiyan Imam. Wannan yana tabbatar mana cewa, masu iko ba cikin cikakkiyar gafala dangane da alakar Imam da mabiyansa na kusa suke ba, a’a, suna  sa ido kan wadannan alakoki, suna kokarin gano su da kuma yin fito-na-fito da su.[11]

Sannu a hankali bangaren fito-na fito  a rayuwar Imam Bakir (a.s) da ta shi’a yana tabbatar da wani fasali na rayuwar Ahlulbaiti (a.s).



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 next