Kaddara Da Hukuncin AllahMufawwada[iii] kuma sun yi imanin cewa Allah ya sallama ayyuka ne ga halittu, ya janye kudurarsa da hukuncinsa da kuma kaddarawarsa daga gare su, da la’akari da cewa; danganta ayyukan gare shi yana nufin dangata nakasa gare shi ne, kuma halittu suna da nasu sababan na musamman duk da cewa dukkansu suna tukewa ne zuwa sababi guda daya na farko wanda shi ne Allah (S.W.T). Duk wanda yake fadin irin wannan magana ta su kuwa, hakika ya fitar da Allah daga mulkinSa ya kuma yi shirka da shi da halittunSa. Abin da muka yi imani da shi a nan muna masu biyayya ga abin da ya zo daga lmamanmu tsarkaka da suke cewa al’amari ne tsakanin al’amura biyu, al’amarin da irin wadannan masu jayayya daga malaman ilimin sanin Allah suka kasa fahimtarsa, wasu kuma suka takaita, wasu kuma suka zurfafa, babu wani daga cikin masana ilimi da ma’abuta falsafa da ya fahimce shi sai bayan karnoni masu yawa. Ba abin mamaki ba ne ga wanda bai tsinkayi hikimar Imamai (A.S) dangane da al’amari tsakanin al’amura biyu ba, ya yi tsammanin cewa wannan magana ta al’amari ne tsakanin al’umara biyu tana daga abin da malaman falsafa na turai na wannan zamani suka gano, alhali kuwa Imamanmu sun rigaye su tun kafin karnoni goma da suka wuce. Imam Sadik (A.S) ya fada yana mai bayanin hanyar nan matsakaiciya da cewa: “Babu Tilastawa kuma babu fawwalawa sai dai al’amari ne tsakanin al’amuran guda biyu.
Wannan kalma ta girmama! Ma’anarta ta zurfafa! A takaice abin nufi shi ne; hakika ayyukanmu a bangare guda ayyukanmu ne bisa hakika kuma mu ne sababinsu na dabi’a kuma suna karkashin ikonmu da zabinmu, a daya bangaren kuma suna karkashin kudurar Allah ne kuma suna cikin karkashin mulkinsa, domin Shi ne mai ba da samuwa mai bayar da ita, bai tilasta mu a kan ayyuka ba ballantana ya zama ya zalunce mu idan ya yi mana azaba a kan sabo, domin muna da iko da kuma zabi a kan abin da muke aikatawa. Kuma bai fawwala mana samar da ayyukanmu ba ballantana ya zamanto ya fitar da su daga karkashin ikonsa ba, al’amarin halittawa da hukuntawa da umarni duka nasa ne, kuma shi mai iko ne a kan komai kuma masani da bayinsa. Ta kowane hali, imaninmu shi ne hukuncin Allah da kaddarawarsa sirri ne daga asiran Allah (S.W.T) duk wanda ya iya fahimtarsa yadda ya dace ba tare wuce gona da iri ba ko kuma takaitawa ba, to wannan ya yi, in ba haka ba, bai wajaba a kansa ba ya kallafawa kansa fahimta da zurfafawa a cikinsa ba, domin gudun kada ya bata, akidarsa ta lalace, domin wannan yana daga al’amura masu zurfi, kai yana daga mafi zurfin bahasosin falsafa wadanda ba mai gane so sai daidaikun mutane, kuma duga-dugan da yawa daga malaman ilimin akida sun zame, kallafa wa kai fahimtarsa, kallafa wa mutum maras ilimi mai zurfi ne da abin da yake sama da ikonsa. Saboda haka ya wadatar mutum ya yi Imani da shi a dunkule kawai yana mai biyayya ga fadin Imamai tsarkaka (A.S) cewa; shi wani al’amari ne tsakanin al’amura biyu, babu tilastawa babu kuma fawwalawa a cikinsa, kuma shi ba ya daga cikin shika-shikan akida ballantana kudurcewa da shi dalla-dalla da zurfafawa su zama wajibi ko ta halin kaka" [1]. Sakamakon Bincike
Dogaro da abubuwan da suka gabata muna iya cewa: kaddarawa da hukuntawa sun kasu gida shida ne kamar haka: Na ilimin Allah (S.W.T) Wannan kuwa mun riga mun yi nuni da cewa ba zamu yi magana kansa ba musamman da yake ya danganta da Palsapa, Na shar’antawa wanda shi ma ba mahallin maganarmu ba ne sai dai mun yi nuni a kai, Sai na uku: na ayyukan bayi da ubangiji a abubuwan da suke faruwa suke wakana, wannan kuwa shi ne mahallin jayayya sosai, kuma a nan ne kafafuwa suke zamewa. A sha’anin samarwa da fararwa da halittawa a fadinmu cewa; Allah (S.W.T) ya halitta, abin nufi a nan ubangiji ne ya kaddara hakan a matsayin samarwa domin cika halitta yadda ya so, kamar ka ce; Allah ya kaddara abin da yake cikin mahaifa ya kasance namiji ne, ko Allah ya kaddara babu yadda za a yi mu ga wani abu sai ta cikin kaloli. Saudayawa ana amfani da wannan a wurare masu yawa; akan ce; Allah ya kaddara dai sai an samu haihuwa tsakanin wance da wane, da nufin cewa; halittawa dai na Allah ne, kuma shi ne yake bayar da haihuwa ga wanda ya so, kuma ya hana wanda ya so, kuma haka nan ne yake tsarawa a samarwa. Amma batun cewa akwai tasirin wasu halittu da idan an kawar da wannan tasirin za a iya haihuwa ko kuma idan aka dauki wani mataki na musamman zai canza yanayin kwayoyin halittar mace domin ta samu ciki wannan ba ya cikin abin da muke nufi a wannan bahasin namu domin yana komawa zuwa ga tasirin sabubban da ake da su kan wasunsu ne, al’amarin da yake nuna mana tasirin da yake tsakanin samammu. Kamar yadda a fadinmu cewa; Allah madaukaki ya hukunta hakan; a nan ana nufin ya riga ya tsara kuma ya kammala halitta din, kamar takarda ce da aka rubuta ta kuma aka sanya hannu kuma aka yi mata sitampin. Don haka idan muka ce: hukuncin Allah haka yake a maganar samun da namiji tsakanin uwaye biyu, to muna nufin ya riga ya zartar kuma ya samar da shi bayan wucewar marhalar tsarawa da daidaita halittarsa a ciki da kuma kammala samuwarsa da cika ta.
|