Kaddara Da Hukuncin Allah



Idan ka ce: Allah ya shiryar da Samudawa wato; ana nufin ya kaddara musu shiriya a shar’ance kenan domin aiko musu annabi (A.S) da ya isar musu da sako. Haka nan ya yalwata musu rayuwa ya tanadar musu duk wani abu da zai kai su ga shiriya ya ba su hankali da zabi da nufi da iko wannan kuwa yana nufin ya kaddara musu shiriya a nau’in halittarsu kenan.

Ya Ubangijin Muhammad da Ali!  Ubangijinmu! girmanka ya daukaka, daukakarak kuwa ba shi da iyaka! kai kadai ne kake iya hada wadannan siffofi, don haka ka shiryar da mu kada ka batar da mu, ka hada siffofin da azahiri ba sa haduwa kuma duka daya ne kuma gaskiya ne, ka batar da adawa kuma ka shiryar da su a lokaci guda! Kuma wannan ayoyi suna nuna mana babban sirrin da yake cikin cewa Allah ba ya tilasta bayinsa kuma suna da zabin kansu. A irin wannan muna iya ganin an samu wani wanda ya hada tanakudin kur'ani a sama da tsawon shekaru ashirin -domin ya nuna yadda Allah madaukaki ya yi ta tanakudi a littafinsa- domin ya rusa sakon Allah, sai ga shi a rana daya ya hadu da imami (A.S), kuma wannan haduwar ta sanya shi ya tuba ya yaga dukkan abin da ya tara kusan rabin karni guda saboda ganin cewa; shi ne bai fahinci maganar Allah ba mai cike da hikima da kamala.

Shin Tilasci Ga Bayi Ya Inganta?

Sai dai mun samu wasu hadisai da suka zo suna nuna cewa Allah ya tilasta bayi a ayyukansu ta yadda ba su da wani zabi kamar ruwayoyi masu cewa: Alkalami ya bushe da abin da zai same ka. (buhari daga abu huraira j 8, shafi 44, bugun alkahira). Da hadisan da suka yi nuni da rubuta komai na ajali da arziki a cikin mahaifiya, ta yadda koda saura zira’i daya ne ya mutu sai ya yi aikin ‘yan’wuta sai ya shige ta. (Buhari, j 8, babin kaddara, shafi: 122). Da hadisan da suke nuna kowane mutum ya yi aiki, domin kowanne an saukake masa abin da aka halitta shi dominsa ne. (Muslim, j 8, shafi: 44). Akwai hadisai masu yawa da suke nuni da hakan, kana iya duba (jami’ul usul, j 10, babin kaddara, hadisi na 7555, shafi: 513. Da ruwayoyi masu cewa: Ubangiji madaukaki ya ce: wadannan suna wuta ba ruwana, wadannan kuma suna aljanna babu ruwana.

Muna iya cewa da an fassara wadannan ruwayoyi da kasancewar wannan a ilimin Allah ne to da sai bahasin ya koma na palsapa sai dai akwai tambayoyi da zasu iya zama a kwakwale kamar cewa; don me wannan ya kebanta da cikin mahaifiya! hada da cewa masu kawo ruwayoyin da masu bayaninsu duk sun fassara shi da fassarar da ba ta nuni da ilimin Allah. Kuma tayiwu wani ya ce: kalmar ciki a nan tana nufin faruwar bawa ta yadda babu ma’ana ga kebantar wannan da ciki, sai kenan ma’anar ciki ta kasance tana nuna mahallin samuwar mutum ne da yana iya kasancewa duniyar barzahu ta farko wato duniyar ZARR (ko kuma duniyar barzahu a gangarowar samuwar rayukan mutane kafin su zo duniya wacce ta saba da ta biyu wacce take a lokacin komawar rayuka zuwa ga Allah madaukaki) ga wanda ya yi imani da ita kenan, domin ilimin Allah bai takaita da ciki ba.

Amma idan muka duba abin da wannan hadisai suke nufi kamar yadda muka yi nuni suna duba ne kai tsaye ga ayyukan Allah mahallici ta yadda zai kai ga tilascin ayyuka da cire wa dan Adam zabinsa da muka yi nuni da cewa hukuncin Allah da kaddarawarsa ba sa cire wa mutum zabin kansa, to sai mu ga wadannan hadisai sun yi hannun riga da koyarwar musulunci da ta tabbata ta ingantacciyar hanya, hada da cewa manyan malamai masana Allah (S.W.T) sun rushe su daga inganci. 

AyatulLahi ja’afar subhani yana fada (Ilahiyyat, shafi 551). “Kai kace kaddara wani abu ne mai hukunci mai kekasar zuci mai wauta maras rahama mai mugun kulli a kan bayi don haka babu wata damar samun rahamarsa madaukaki da kyautatawarsa”. A dai wannan shafin yana fada cewa: “Wadannan ruwayoyin sun saba da abin da ya zo a kur’ani da sunna domin littafin kur’ani yana nuna dan Adam a matsayin wani halitta ne mai zabin kansa, kuma shiriyarsa da batansa suna wuyansa”. Sannan sai ya kawo ayoyi kamar fadinsa madaukaki:

“Mu mun shiryar da shi tafarki, imma dai ya kasance mai godiya ko mai yawan butulcewa”. Insani (Dahari: 3). Da fadinsa madaukaki: “Ka ce idan na bata kawai ina fatar da kaina ne, idan kuma na shiriya to sakamakon abin da Ubangijina yake yi mini wahayinsa ne, hakika shi mai ji ne makusanci”. (Saba’: 50). Da fadinsa madaukaki: “Hakika hasken shiriya sun zo muku daga Ubangijinku, duk wanda ya ga hanya (shiriya) to ga kansa ne (amfanin yake) wanda kuwa ya makance (ya bata) to yana kansa ne…” (An’am: 140).

Ina ganin akwai maganganu masu yawa game da wannan da magana kan su yake tsawaita, kuma a cikin abin da muka kawo a takaice akwai isarwa ga wanda ya kasance yana neman tunatarwa, ko kuma wanda yake da zuciyar lura ya sanya idanuwansa da kunnuwansa na basira. Allah ka taimaka mana shiriyar kanmu kada ka tabar da mu da batan kanmu.


[1] Aka’idul imamaiyya babin kadhaa wa kadar.

[2] Tauba: 115

[i] Su ne mutanen da suka tafi a kan cewa ayyukan bayi a bisa hakika ayyukan Allah ne ba tare da wani tawili ba a kan haka, don haka Allah (S.W.T) shi ne yake aikata ayyukan bayi kai tsaye.

[ii] Mujabbira, da Ash’ariyya suna da wannan ra’ayi da aka san shi da jabar na musun wasida tsakanin Allah da ayyukan da ya halitta ba. Sun musa abin da ya sanya shi tsakaninsa da bayinsa da falalarsa. Misali kamar ‘ya’yan mangwaro da suke zuwa daga itace, sai suka ce kai tsaye Allah ne ya halitta su ba tare da wata rawa da shuka a matsayinta na wasida ta taka ba, wannan shi ne kwatankwacin ayyukan bayinsa a wajansu, don haka kai tsaye ayyukansu ayyukansa ne.

[iii] Mu’utazilawa sun saba da Mujabbira da Ash’ariyya, su sun tafi akan Tafwidi da ma’anarsa take nufin cewa; babu hannun Allah a cikin ayyukan bayi ko kadan, wannan ra’ayi da shi da na farkon duka a gun mazhabar imamiyya kuskure ne.

[iv] Idan muka gane ma'anar kaddarawa kamar yadda ya gabata zamu samu cewa; a sharia'nce Allah yana kaddarawa, kamar yadda ya kaddara cewa mu yi salla dare da rana guda biyar, ko kuma mu yi azumin watan Ramadan, ko kuma mu yi zakka mu bayar da humusi, ko kuma mu yi horo da kyakkyawa mu yi hani ga mummuna bisa sharuddan kowanne daga hukunce-hukuncensa kamar yadda suka zo a littattafai.

 



back 1 2 3 4 5 6 7 8