Kaddara Da Hukuncin Allah



Abdullahi dan umar ya ruwaito daga Abubakar halifa na farko (a cikin tarihin hulafa, na suyudi) cewa: wani mutum ya zo wajen Abubakar sai ya ce masa: shin kana ganin zina kaddarawar Allah ce? sai ya ce: E. Sai mutumin ya ce: Kana ganin Allah ya kaddara mini sannan sai ya azabtar da ni? Sai halifa Abubakar ya ce: Ya kai dan kaskantacce da akwai wani mutum a kusa da ni da na umarce shi ya fasa maka hanci.

 AyatulLahi Subhani yana cewa: “Wannan mutumin ya fahimci cewa; kaddarar Allah da kuma sakamakon azaba a kan aiki ba su dace da adalcin Allah madaukaki ba, kuma wannan yana nuna kenan dole ne a jefar da daya daga ciki, kuma Halifa da ya kasa bayar da amsa mai gamsarwa a wannan mas’ala ga wannan mutumin sai ya yi gargadi da barazana kawai, kuma wannan yana nuna mana a fili cewa: a kwakwalen wasu mutane kaddarar Allah tana daidai da tilastawarsa ne”. (Ilahiyyat shafi: 509).

Idan mun duba zamu ga wannan mutumin yana ganin Allah ya kaddara masa yin zina a ayyukansa wanda wannan al’amari ne da yake komawa zuwa samuwarsa, sannan kuma sai ya kaddara masa kuma ya hukunta masa haramcinta wanda al’amari ne da yake na shar’antawarsa, sannan kuma sai ya azabtar da shi idan ya yi, wanda yake komawa ga ayyukan Ubangiji na samarwa.

Kuma muna iya ganin wannan a fili yayin da Umar dan Khaddabi halifa na biyu ya gudu a yakin Hunain, sai Ummul Haris al’ansariyya ta gan shi yana gudu sai ta tambaye shi lafiya dai?! Sai ya ce: Al’amarin Allah ne: wato kaddarawar Allah ce. (Almagazi na alwakidi). A nan muna iya gani a fili yake cewa; Allah ya shar’anta wa musulmi su kare kansu daga sharrin makiya kuma al’amari ne na shar’ia, amma halifa kuma ya danganta gudunsa wanda yake abu ne na samarwa da yake komawa zuwa ga ayyukansa da cewa shi ma kaddarawar Allah ce. Sai ya kasance Ubangiji ya kaddara masa ya je yaki a ayyukansa, kuma ya shar’anta masa tafiya yakin, sannan kuma sai ya kaddara masa ya gudu.

Banu umayya su ne farkon wadanda suka karfafi wannan al’amari a kwakwalen mutane domin su ci karensu ba babbaka, su yi zalunci yadda suka so sai kuma su danganta shi ga Allah, wannan al’amari yana da bayanai masu yawa a tarihi da ba zamu iya kawo su a nan ba.

Ayyukan mutum kai tsaye sun saba da maganar halittawa, a nan ne ya kasance mahallin da dan Adam ba shi da tilasci daga Allah, da wannan ne muke iya sanya mutum tsakanin kolum biyu da shi da mala'ika da aljani domin su ne mahallin maganar Allah a wannan wurin, kuma su ne wadanda suke iya sabawa ko su yi biyayya. Da mala'ika ko aljani ko mutum ya ga dama yana iya bin Allah ko kuma ya saba masa bisa daidai ikonsa da zabinsa da Allah ne ya halitta shi da shi, kuma haka Allah da hikimarsa maras iyaka da misali ya hukunta.

A nan ne mahallin da ake cewa Allah ya hukunta amma ba ana nufin bisa tilasci ba, kamar yadda ake cewa ya hukunta amma ba ana nufin ba shi da hannu a ciki ba, a nan Allah bai yi duka biyun ba, bai tilasta ba, kuma bai cire hannunsa ba, domin idan ka ce ya cire hannunsa to a nan ka bi ra'ayin mu'utazilawa, kamar yadda idan ka ce ya tilasta ka bi ra'ayin mujbira da ash'arawa da kuma ma'abota sufanci.

A nan ne Ahlul Baiti (A.S) suke karfafawar cewa: al'amarin tsakanin wadannan abubuwa biyu ne: Idan ka ce Allah ya hukunta ko kuma ya kaddara ko kuma ya so ko ya zartar da cewa; a haife ka bahaushe ko bature ko balarabe to wannan yana komawa ne zuwa ga na farko wato halittawa da ba ka da iko a kai sai yadda ya yi ka, ya sanya ka da ga bahaushe ko ba'amurike ko bature, ko balarabe, ko makamancin hakan. To a nan yana nufin ya tilasta ka tayadda ba ka da wani zabi, daidai kake da wanda aka daure hannayensa aka jefa ruwa, a nan ko ka ki ko ka so dole ne ka jike.

Amma idan ka fadi cewa; Allah ya hukunta ko kuma ya kaddara ko kuma ya so ko ya zartar da cewa ka kasance musulmi ko kirista ko bayahude ko arne ko bamajuse to a nan ya saba da fadin ka na sama, domin a nan yana nufin Allah ya umarce ka da ka bi hanyarsa sai ka bi ko ka ki bi, don haka sai ka bi shi ka kasance musulmi ko kuma ka ki bin sa sai ka kasance bayahude ko kirista ko arne ko kuma bamajuse. A nan ne muke cewa da ya tilasta ka, da aiko manzanni da sako da sanya wasiyyai domin shiryar da dan adam ya zama wasa kenan, da hadafin aiko sako ya kasance barna da wasa. Don haka wannan ya faru ne da zabika, kuma a kan haka ne mazhabin Ahlul Baiti (A.S) ya saba da mujabbira da asha'arawa da kuma kirista da yahudawa da masu sufanci (sufancin da ya saba wa koyarwar tafarkin Ahlul Baiti (A.S).

Kai yahudawa sun zurfafa a kan cewa; ba ma kawai ya yi wa dan Adam tilas ba, shi kansa ya yi wa kansa tilas ba zai iya canja abin da ya dora wa kansa ba kamar yadda suke cewa; “hannayen Allah abin yi wa kukumi ne”, wato ya riga ya zartar dole ne a kansa ya yi kaza kuma ba zai iya iya canjawa ba, wannan kuwa ya yi tasiri har a shari'arsu da suke cewa mustahili ne a samu shafaffen hukunci domin an riga an gama.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 next