Hakkokin Soyayya



309. Daga al’kafi, daga sa’id dan Hasan ya ce: Abu Ja’afar (A.S) ya ce: Shin dayanku yana zuwa cikin aljihun dayanku sai ya sanya hannunsa ya dauki abin da yake bukata shi kuma ba ya hana shi? sai na ce: ban san wannan ba a cikinmu. Sai Abu Ja’afar (A.S) ya ce: ashe ba (kwa) komai. Sai na ce: ashe mun halaka kenan! Sai ya ce: har yanzu ba a ba wa mutane hankulansu ba kenan (wato hankulansu ba su cika ba).[17]

i- Zabar Wani A Kan Kai

310. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: ka kaunaci masoyinka ya kaunace ka, ka girmama shi ya girmama ka, ka kuma zabe shi a kan ka ya zabeka a kansa da iyalinsa[18].

J- Kiyaye Wanda Ba Ya Nan

311. Daga Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: ku tuna da dan’uwanku idan ba ya nan fiye da yadda kuke son a tuna da ku idan ba kwa nan[19].

k- Yafe Kurakurai

312. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: mafificin ‘yan’uwanku shi ne wanda ya yafe muku aibobinku [20]

313. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: hakika dayanku madubin dan’uwansa ne, idan dayanku ya ga cuta (kazanta) gareshi to ya kawar masa da ita[21].

314. Daga Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce mafi soyuwar dan’uwana gareni shi ne wanda ya yafe mini aibobina[22].

L- Yin Addu’a A Bayan Ido

315. Al’kafi daga Ibrahim dan Hashim: Na ga Abdullahi dan Jundub a wasu wurare ban ga wani aiki da ya fi aikinsa ba, bai gushe ba yana addu’a yana mike da hannayensa zuwa sama kuma hawayensa suna zuba kan kumatunsa har sai dai ya kai kasa. Yayin da mutane suka tafi sai na ce masa: ya kai abu Muhammad, ban ga wani abu mafi kyawu daga abin da ka yi ba. Sai ya ce: wallahi ban yi addu’a ba sai ga ‘yan’uwana; wannan kuwa saboda abulhasan Musa (A.S) ya ba ni labari cewa wanda ya yi addu’a ga dan’uwansa bayan idanuwansa za a kira shi daga bayan al’arshi: “kana da ninki dubu dari na hakan” sai na ki in bar dubu dari mai tabbas saboda daya da ban sani ba za a amsa ta ko kuwa[23].

M- Hani Ga Mummuna

316. Daga Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: wanda ya ga wani abu da yake ki daga dan’uwansa kuma bai hana shi ba –yana da ikon yin hakan- to hakika ya ha’ince shi[24].

N- Yafe Kurakurai

317. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: -a ambaton siffofin mumini- shi mai tausasawa ne ga dan’uwansa a kan kuskurensa, kuma yana kiyaye abin da ya gabata na tsohuwar abotarsu[25].

318. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: ka jurewa kurakuran mai sonka na wani lokaci, saboda (maganin) harin makiyinka[26].



back 1 2 3 4 5 6 next