Hakkokin Soyayya



c- Yin Nasiha

299. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: mumini dan’uwan mumini ne, kada ya bar yi masa nasiha takowane hali[7].

d- Taimakawa

300. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: wanda ya taimaki dan’uwansa musulmi yana ikon yin hakan, to Allah zai taimake shi a duniya da lahira.[8]

301. Daga Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: babu wani mumini da zai ki taimakon dan’uwansa kuma yana da ikon ya taimaka masa, sai Allah ya kaskantar da shi a duniya da lahira[9].

e- Taimakekeniya

302. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: idan so ya kafu, to wajibi ne a zowa juna a kuma yi taimakekeniya[10].

303. Daga Imam Muhammad Bakir (A.S) ya ce: wanda ya yi rowa da taimakonsa ga dan’uwansa musulmi da tsayuwa gareshi a cikin biyan bukatunsa, to za a jarrabe shi da taimakon wanda sabo ne taimakonsa kuma babu wani lada[11].

f- Biyan Bukatu

304. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: muminai ‘yan’uwan juna ne, sashensu yana biyan bukatun sashe, kuma ta hanyar sashensu ya biya bukatun sashe ne Allah yake biyan bukatunsu ranar kiyama[12].

g- Girmamawa

305. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: wanda ya girmama dan’uwansa musulmi da wani mazauni da yake girmama shi da shi, ko wata kalma da yake tausasa masa da ita, ko wata bukata da ya isar masa da ita, to ba zai gushe ba a inuwar mala’iku matukar yana wannan matsayin[13].

306. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Babu wani bawa a al’ummata da zai tausasa wa dan’uwansa saboda Allah da wani ludufi sai Allah ya yi masa hidima daga hadiman aljanna[14].

307. Daga Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: wanda ya girmama addinisa zai girmama ‘yanuwansa, wanda kuwa ya wulakanta addinisa to zai wulakanta’yan’uwansa[15].

h- Taimakawa (da dukiya)

308. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: ka bayar da dukiyarka ga hakkoki kuma ka taimaki aboki da ita; ka sani kyauta ga da ita tafi[16].



back 1 2 3 4 5 6 next