Gudummuwar Ahlul Baiti (A.S)



4- Kamanta jagoranci na kamalar mutumtaka a ayyukan daidaikun mutane da na al’umma.

5- Kariya ga musulunci (akidar musulunci, tsarin siyasar musulunci).

6- Kariya ga al’ummar musulmi, da kuma kare samuwarta da abubuwan da suka kebancetga da kadaitakarta (zamanta na al’umma daya).

7- Gina al’umma ta gari da gina mutane tsarkaka zababbu wadanda suke iya daukar nauyi na musamman.

Kafin haka muna bukatar bayanin nazarin jagorancin Ahlul Baiti (A.S) a cikin sakon musulunci da ya tattara dukkan abubuwan wannan daurori da muhimman al’amura, da kuma dalilin kebantar wannan al’amari a sakon musulunci da su?.

Ba makawa wannan aiki da wannan fadi yana bukatar lokaci yalwatacce isasshe da kuma dama da ta dace da mutane masu taimakawa isassu.

Sai dai ni na samu kaina mai tunkuduwa da izuwa zuwa ga wannan aiki domin har abada aiki na gari abin dogarawa ga Allah ne da kuma neman taimako daga gareshi, ina mai kaunar dacewa da ikhlasi na niyya da gaskiya da shiriya daga Allah a cikin wannan aiki “wanda ya dogara ga Allah to shi ya isar masa hakika Allah mai isar da al’amarinsa ne hakika Allah ya sanya wa komai iyaka”[3].

Kamar yadda na samu kaina abin turawa zuwa ga farawa da hadafi na bakwai wato shi ne jama’a ta gari, ta yiwu dalilin zabar wannan shi ne abin da na ke ji na bukatuwa a aikce a yanzu ga samar da sura cikakkiya game da al’umma ta gari, domin ya zama misali na hakika da kuma gabatar wa masu aiki a fagen aiki na siyasa da zamantakewa da suke koyi da shi suke kuma koyi da shiriyarsa.

Kamar yadda wannan bincike da yake cike rara da gibi a tsarin karatu na daliban ilimin addini, kamar yadda yake mai amfani ga masu huduba da masu tabligi, da kuma gun wayayyun mutane muminai a kasashen musulunci, ko a wajan hijira ko a kasashen bakunta, wadanda ba kasafai sukan samu iko a kan sanin bayanai cikakku ba game da wannan al’amari.

Kuma duniyarmu ta musulunci ta ga wannan cigaba mai yawa a wadannan fagage na hauza da tabligi da kuma fuskantowar masana da tunani gamamme game da musulunci, da hijira zuwa kasar yamma. Ta yadda irin wannan littafi zai tanadi mafi yawan sakonni na gaba daya da suke bukatarsa a hirarrakinsu cikin al’umma da kuma tattaunawa game da Ahlul Baiti (A.S) da jama’a ta gari.

Kafin haka ni a kan kaina na kasance ina jin akwai bukata mai karfi ta gabatar da irin wannan misali a waje ga jama’a ta gari da muke ta hankoron samar da ita da kuma dabbaka ta. Domin nazarin musulunci ya zama ya dabbaku a fili, ba kawai ya zama tunani da kaddarawa ba ta hadamar duniyar sha’awa, da karo da junan maslahar duniya da kuma tanakudin siyasa da kuma takurawar nan ta rai da duniyarmu a yau take rayuwa a kai.



[1] - Surar Ahzab: 23.

[2] - Hukumar Saddam Aflaki Tikriti ta kashe shi a shekarar (1400h. 1980m) tare da yar’uwarsa mai girma alawiyya sidiya Bintul huda haka kawai ba tare da wani zunubi ba da ya yi ba sai dai kawai don sun ce: Allah ne ubangijinmu sannan suka daidaitu a kan hakan, kamar yadda kafin kashe su da bayan kashe su ya kashe dubunnan gomomin muminai na gari, a kokarin azzalumi na kawar da gaba dayan samuwar musulunci a I raki da ya dauki lokaci sama da shekara goma sha bakwai zuwa yanzu.

[3] - Talak: 3.

 



back 1 2 3 4 5 6