Gudummuwar Ahlul Baiti (A.S)



Hakika Ahlul Baiti (A.S) yayin da suka zama fikira da kuma bayani na sakon karshe, ba makawa a kan haka mu kaddara cewa su suna aiki ta mahanga daya ne na tunani da kuma abubuwan da suka shafi tafiyar da rayuwar zamantakewar al’umma da ya shafi maslaha ko barna, da kuma matakai da suke da alaka da hakan, su a wannan fage kamar annabawa suke da ake cewa da zasu hadu a zamani daya da ba a samu sabani ba a ra’ayoyinsu da zantuttukansu da ayyukansu da matsayansu.

Amma duk da haka zamu samu cewa akwai sabani bayyananne a wasu lokuta a yanayi da surar wadannan matakai, wani lokaci a maganganu ko a aiki ko a tafarki da usulubi kamar yadda yake ga annabawa kansu, ashe kenana menene ma’auni guda daya da zamu iya fitar da hukunci daga zantuttukansu da ayyukansa da mtsayansa da sulukinsu ta hanyarsu? Ta yadda zamu iya samar da nazari daya wanda zamu iya fassara dukkan wadannan sabanin bisa asasinsa, kamar yadda zamu yi la’akari da hakan a kur’ani mai girma yayin da yake magana game da annabawa.

Ba makawa cewa abin da malaman musulunci mabiya koyarwar Ahlul Baiti (A.S) suka yi riko da shi suka kuma tsayu a kan sa, hada da nassosin da suka zo daga Ahlul Baiti (A.S) domin su warware dukkan wadannan al’amuran, zai iya yiwuwa su shakkala asasi da kuma madogara duk yadda aka samu canji ko cigaba a irin wadannan al’amuran.

Ta yiwu daya da ga cikin wadannan cigaba a bincike game da Ahlul Baiti (A.S) wanda ya shafi wannan bincike shi ne abin da malaminmu masanin musulunci, mai ilimi, mai girma Ayatul-Lahil uzma shahid Muhammad Bakir Sadar ya fara a kan abin da ya rubuta game da Ahlul Baiti (A.S), sai dai wadannan bincike ba a rubuta su ba cikakku a yanayinsu da kuma adadinsu, bayan munanan hannaye na ta’addanci a bayan kasa sun kashe shi[2].

 Wannan bincike bisa dabi’arsa yana bukatar share fage mai fadi muhimmi, da ya ke kunshe cikin littattafan Ahlul Baiti (A.S), da ya shafi bahasin fikira da tarihi da akhlak da akida, da aka gada daga Ahlul Baiti da kuma yake a warwatse cikin littattafan hadisai da tafsiri da akhlak da addu’a da ziyara.

Duk da cewa akwai cigaba a binciken bahasin Ka’idoji da usul da suka dogara a kanta ta wata nahiya, haka nan kuma wannan bincike game da abubuwan da suka bari na gado daga garesu (A.S) da muka ambata a sama ya samu daskarewa da kwantai da jumudi, bai samu cigaba ba kamar yadda ya samu a gwargwadon bahasin Fikihu da Usul da Rijal.

Bayan haka bahasin nazari a kan hakan ya dogara a kan doka ta farko da aka cakuda mai kyau da maras kyau, da mudlak da mukayyad, da Amm da Khas, da Muhkam da MutashAbuh, da Mujmal da Mubayyan…..da makamantansu.

Ko kuma bahasin ya dogara a kan sakamkon bincike na ilimi da malamai wadanda suka gabata suka kai zuwa ga reshi, wanda shi sakamako ne na ijtihadi na ilimi, sannan aka fitar da hukunci daga gareshi ta hanyar bayani dalla-dalla.

Ko kuma mai bincike ya tsayu da ijtihadi na musamman da ba ya iya yiwuwa ga daidaikun mutane, domin bincike don samar da wata mahanaga game da wannan maudu’i.

Sasannin bincike a wannan bayani na Ahlul Baiti (A.S)

 Sai dai ni na samu kaina -tare da dukkan wahalhalu da suke tattare da wannan maudu’i- kafin shekaru masu yawa gaban wannan kokari mai sauki na rubutu a wannan janibi na nazari, wannan ko ya faru yayin da majma’al alami li Ahlil Baiti (A.S) ya tsayu da kokari da kulla mu’utamar da ya shafi duk fadin duniya ta yadda na rubuta wasu makaloli da na yi kokarin jefa wasu sashen mahangai da ra’ayoyi na gama-gari game da shi sai na samu karfafawa da godiya daga wasu masu bayar da gudummuwa a wannan mu’utamar.



back 1 2 3 4 5 6 next