Gudummuwar Ahlul Baiti (A.S)



Sai na ga yana daga cikin muhimmin abu shi ne in fara ko in cigaba da rubuta wannan bahasi da bincike, sannan nan gaba muna fatan a samu wasu malamai da masu bincike su kammala shi.

 Duk da cewa akwai yawan shagulgula da jarrabawoyi da ayyuka da aka jarrabce ni da su a wannan lokaci na rayuwata, wacce take ba zata yi daidai da samun lokaci isasshe domin ayyuka na sakafa ba, sannan akwai ma abubuwan da sukan iya hana hakan bisa al’ada, da kuma nisanta ta daga fagen ayyuka na ilimi na hauza da yanayinta da hidimarta, sai na ga bari in yi kokarin komawa da wannan muhadara da kuma bayaninta, sai na bude sasanni masu dama na bincike.

Na farko:Bayanin hadafin asali domin samar da bayani game da Ahlul Baiti (A.S) a sakon karshe, ta yadda wannan bincike zai yi bayani game da rukuni mafi girma na manzancin musulunci. Wannan kuma zai kasance akawai bangare da aka yi tarayya tsakanin imaman Ahlul Baiti (A.S).

Na biyu: Bayanin matakai da kowanne daga cikin imamai (A.S) ya kebanta da shi a zamaninsa a marhalarsa da kuma alakar da take tsakanin wancan matsayi da dayan da kuma alakarsa da hadafi na asali, dukkan wannan tare da kashe-kashen tarihin Ahlul Baiti (A.S) zuwa marhaloli daban-daban, da bayanin abin da ya kebanci kowace marhala.

Na uku: Binciken al’amura na tunani da akida da shari’a da mazhabar Ahlul Baiti (A.S) ta kebanta da su ta nahiyar alakarta da nazarin musulunci a gun Ahlul Baiti (A.S) da sanin cewa wannan bincike a wadannan al’amura ta nahiyar kalam da fikihu yana daga binciken da malamanmu suka yi bayani cikakke akai.

Na hudu: Tafarkin mabiya Ahlul Baiti (A.S) bayan gaibar (fakuwar) imami (A.S) da kuma matakan da suka bi suka wuce takai, da kuma rawar da suka taka wajan daukar mas’uliyya mai girma da take da alaka da nazari kan marja’iyyar addini ta gari.

Gudummuwar Ahlul Baiti (A.S) A Rayuwar Musulunci

 Sai na samu cewa bahasi na farko yana bincike ne game da asasi wanda yake kunshe da bahasosi masu muhimmanci a nazari da kuma aiki, ta yaddda kowane daya daga wadannan hadafofi suna bukatar littafi na musamman ta yadda za a iya takaita wadannan bayanai na hadafofi daga bayanin muhimmancin rayuwar Ahlul Baiti (A.S) da wadannan bayanai masu zuwa kamar haka:

1- Kafa hujja a kan mutane da shaida a kan ayyukan mutane.

2- Halifanci na ubagiji, ko shugabanci, ko jagorancin hukumar musulunci.

3- Marja’iyya ta tunani da addini ga musulmi.



back 1 2 3 4 5 6 next