Ayyuka da Sakamako



A nan ya kamata mu yi bayani a kan wadannan ruwayoyi kamar haka. Wani lokaci wasu mutane ba tare da sun yi alkawari ba zasu yi wasu ayyuka na kwarai, sannan su bayar da ladar wadannan ayyukan zuwa ga wadanda suka riga mu. Babu shakka duk lokacin da mutum ya yi wani aiki na kwarar kuma saboda Allah, tabbas zai samu ladar wannan aikin daga Ubangiji a matsayin baiwa ta Allah madaukaki ba wai don ya cancanci hakan ba ne, amma Allah madaukaki ta hanyar wannan baiwar yake bayar da ladar ayyuka. Sannan ta hanyar wadannan ruwayoyin mun fahimci cewa Allah madaukaki ya bayar da damar cewa ana iya yin ayyukan lada a madadin wadanda suka riga mu sannan a yi kyautar ladar zuwa garesu.

Bakance Da Waliyyan Allah

Musulmai sakamakon soyayya ta musamman da suke da ita ga Manzo da iyalansa tsarkaka, wani lokacin domin samun kusanci zuwa ga Ubangiji sukan yi alkawarin wani abu zuwa ga waliyyan Allah, ta yadda yayin da zasu yi wannan bakance zasu ce na yi wa Allah alkawarin kaza, amma wannan ba zai hana ladar ta je wa Manzo da waliyyan Allah ba.

Tare da la’akari da wannan zamu gane ma’anar wannan jumla “Na yi Alkawari zuwa ga Allah zan yanka rago ga annabi ko wanda ya yi mini wasiyya”. A nan dole a lura da kalmar Allah ba tana bayar da ma’anar kalmar Annabi ba ce.

A cikin wadannan kalmomi guda biyu duk da cewa akwai wadansu abubuwa masu kama da juna amma ba daya suke ba, domin kuwa ga yadda abin ya zo a cikin harshen larabci “Lillahi alayya an azbahu shatan linnabiy” lamun din da ya zo a cikin kalmar “Lillahi” yana nuna neman kusanci ga Allah ne, amma lamun da ya zo a cikin kalmar “linnabiy” yana nuna wanda aka yi aikin don shi ne, sannan cikin sa’a duka wadannan lafuzan guda biyu sun zo a cikin Kur’ani mai girma kamar haka:

Dangane da wannan ga abin da Allah yake cewa: “Ka ce ni ina yi muku wa’azi ne da abu guda daya shi ne ku tsayar da salla domin Allah (Lillah).

A cikin wata ayar kuwa yana cewa: Lallai sadaka saboda mabukata ce (lilfukara).

Saboda haka bai kamata ba a dauki wannan wani abu na hada Allah da waninsa wato shirka, don mutum ya ce na yi niyyar yanka wannan domin Manzo, wato ma’anarsa shi ne na yi wannan ne saboda Allah kuma ladar zuwa ga Manzo. Saboda haka ma’anar jumlar “Lillahi, linnabiy” shi ne na yi wannan aiki ne ladarsa zuwa ga Manzo don neman kusanci zuwa ga Allah. Sannan irin wannan ya zo a cikin hadisin Ubada da ya gabata inda yake cewa na gina wannan rijiya ne (li'ummi) wato dan mahaifiyata. Ma’aunin shi ne niyyar da aka yi aikin ba zahirin aikin ba.

Masu hadisi sun ruwaito daga Manzo (s.a.w) yana cewa: Lallai ayyuka suna tare da niyyar da aka yi su tare da ita. Tare da la’akari da ma’anar wannan hadisi dole ne mu bambance wani aiki da mai kadaita Allah zai yi, kamar ya yanka wata dabba domin Manzo (s.a.w) a matsayin bakance, da wanda wani mushiriki zai yanka wata dabba ga gumakansu, duk da cewa wadannan abubuwa guda biyu sun yi kama da juna amma akwai gayar bambanci idan muka lura da badininsu, kuma ba za a taba daidaita su ba.

Mutumin da yake kadaita Allah ya yi alkawari ne ya yanka wani abu zuwa ga Allah, kuma ya yi wannan yanka ne domin ya samu lada daga Allah. Amma mushrikai suna yanka wadannan abin yanka nasu ne da sunan gumakansu, kuma suna neman lada ne daga gumakan nasu. Saboda haka ta yaya za a iya daidaita wadannan ayyuka guda biyu? Idan har ya zamana zahirin aiki shi ne ma’auni wanda zai yi hukunci a kansa, to zai zama aikin hajji ya yi kama da aikin mushrikai, domin kuwa suna zagaya gumakansu ne suna bautarsu, muma kuma muna zagaya dakin ka’aba muna yin dawafi kuma muna sumbatar Hajrul aswad. Sannan suna yanka ragunansu a mina da sunan gumakansu, muma muna yanka ragunammu na hadaya a wannan rana, amma shin wadannan ayyukan guda biyu zasu zama daya?

Abin da yake sanyawa masu bautar gumaka suna bauta musu shi ne, neman yardarm gumakan, amma abin da yake sanyawa mumini yake bauta shi ne neman yardar Allah. Mai kadaita Allah yana bayar da kyautar ladar yankansa zuwa ga annabi da waliyyan Allah, sannan ruwayoyin suna nuni ga ingancin hakan.

Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com – www.hikima.org

Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)

Facebook: Haidar Center - December, 2012



 



back 1 2 3 4 5 6