Ayyuka da Sakamako



Ayyuka Da Kyakkyawan Sakamako

 

Mawallafi: Ayatullahi Ja’afar Subhani

Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani

Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id

A sakamakon bincike na ilimi da falsafa an tabbatar da cewa mutuwa ba ita ce karshen rayuwar dan Adam ba, mutuwa kawai cirata ce daga wata duniya zuwa wata domin ci gaba da rayuwa, don haka hakikanin dan Adam ba shi ne jikinsa ba, ta yadda sakamakon lalacewarsa ya zamana mutum ya kau, hakikanin dan Adam shi ne ruhinsa kamar yadda muka tabbatr a baya, wanda sakamakon mutuwa ba zai kau ba, zai ci gaba da rayuwa a wata duniyar ta daban da wani jikin da ya dace da shi, wanda malamai suka ambata da “barzakh”.

Sakamakon mun yi cikakken bayani a kan wannan magana a nan ba sai mun sake Maimaitawa ba, yanzu abin da muke magana a kansa shi ne, shin wai wadanda suka rigamu gidan gaskiya suna iya amfana da wasu ayyukammu ko kuwa ba zasu amfana ba.

Da wata ma’nar shin idan muka yi wani aiki mai kyau a matsayin kyauta ga ruhin iyayemmu wadanda ba su raye a wannan duniyar, shin zai yi amfani a gare su kokuwa?

Dangane da wannan magana dole ne mu koma zuwa ga Kur’ani da hadisi domin mu samu amsar wadannan tamabayoyi da muka ambata daga tushen addini wato Kur’ani da sunnar ma’aiki (s.a.w).

A baya mun yi tunatarwa da cewa imani ba tare da aiki ba, ba zai amfanarba, sakamakon haka ne ya zamana ayoyi suna bayanin imani tare da aiki da wannan jumla kamar haka: “Wadanda suka yi imani suka kuma yi aiki kyakkyawa”. Wannan jumla ta zo a wurare daban-daban a cikin Kur’ani. Don haka mutum ba zai iya dogara da imaninsa ba kawai ba tare da aiki ba, ko kuma da dogaro da cewa idan na rasu dana zai yi mini aiki mai kyau a bayana, don haka tsirar mutum tana tare da imaninsa da aiki mai kyau.



1 2 3 4 5 6 next