Ayyuka da Sakamako



A karshen karni na farko da farkon karni na biyu aka samu wasu gungu masu suna “Murji’a” wadanda kawai suke dogara da yin imani, ba tare da dogaro ba a kan yin aiki, shugabannimu sun soki wannan ra’ayi sannan iyayemmu da kakannimmu suna horan mu da cewa mu yi wa ‘ya’yanmu tarbiyya kafin su fada tarkon “murji’a”.[1]

Tunanin ceto wanda ake jingina shi zuwa ga iyalan gidan Manzo wanda ba tare da kokari wajen yin aiki ba, wani tunani ne wanda ba da shi tushe. Wannan tunani ya samo asali ne daga yahudawa, wadan suka dauki kansu a matsayin al’umma mafificiya, sannan suka dauki kansu cewa su ‘ya’yan Allah ne, sakamakon haka ne suke kore duk wani nau’i na zunubi daga kawunansu, sannan tunaninsu shi ne cewa: “mu ‘ya’yan Allah ne kuma wadanda suke sonsa”[2]

Daga wannan bayanin zamu fahimci cewa tsirar mutum kawai ta rataya ne ga ayyukansa kyawawa, don haka dogara da ayyukan wani ko jingina kai ga wasu abubuwa mararsa tushe tunani ne wanda ba shi da inganci kuma sam bai kamata a dogara a kansa ba.

Amirul mumininn Ali (a.s) dangane da aiki yana da wasu jumloli masu kawatarwa a kan karfafa batun aikin, wanda a nan zamu kawo guda biyu kawai daga cikinsu kama haka:

1-“Ku sani yau rana ce ta aiki babu hisabi, gobe kuwa rana ce ta hisabi babu aiki”[3].

2-Ku sani yau rana ce ta koyo, gobe kuwa rana ce ta gasa, wanda layin karshe na wannan gasa shi ne aljanna, wanda ya kasa kaiwa kuwa makomar shi ita ce jahannama, shin akwai wani daga cikinku wanda zai tuba daga laifukansa kafin mutuwa ta riske shi, shin akwai wanda zai yi aiki kafin ranar kaico ta riske shi”.[4]

Tare da imani da wannan asali shin akwai sauran Bahasi kuma a kan cewa, shin wadanda suka riga mu zasu iya amfana daga ayyuka kyawawa da muke yi, misali kamar idan muka yi wani aiki a mai makonsu zasu iya amfana da wannan aiki namu?

Muna bukatar amsar wannan tambaya daga Kur’ani da sunnar Manzo wanda zamu ga cewa tabbas amsar wannan tambaya shi ne tabbas zasu iya amfana.

Kafin mu ci gaba da bayani kan wannan al’amari zamu yi tunatarwa a kan cewa ayyukan mutum a mai makon wani sun kasu zuwa gida biyu:

1-Wani lokaci mutumin da ya rasu yana da hannu wajen ayyukan wanda yake raye.



back 1 2 3 4 5 6 next