Kamun kafa Da Annabawa Da Waliyan Allah



2- Kusanci zuwa wajen Allah.[12]

3- Samar da abubuwan da zasu kusantar da mutum ta yadda zai samu kusanci zuwa ga Allah.[13]

Tabbas ma’ana ta farko ba ita ake nufi ba a nan, domin kuwa matsayin da Manzo yake da shi a wajen Allah babu wanda yake da shi, kuma babu wanda zai samu kamarsa. Saboda haka dole ne mu fassara wannan aya da daya daga cikin ma’anoni biyu na karshe, kuma ga dukkan alamu wannan aya tana daukar ma’ana ta uku ne, domin kuwa abin da yake tabbatar da hakan bayan an yi umarni da neman tsani, yana yin umarni da jihadi wanda yana sanya kusanci zuwa ga Allah. Sannan wannan ya zo a cikin hadubar Imam Ali (a.s) wanda ya dauki ma’anar tsani da cewa shi ne riko da abin da zai kusantar da mutum zuwa ga Ubangiji, inda yake cewa: Mafificin abin da masu neman kusanci zuwa ga Allah zasu nemi kusanci zuwa gare shi, shi ne yin imani da shi, da manzonsa da yin jihadi a tafarkin Allah, sannan da tsayar da salla domin kuwa hanya ce kuma shari’a ce, sannan fitar da zakka.

A cikin wannan huduba ta Imam yana kawo wajibai na shari’a wanda yake nuna cewa su ne suke kusantar da mutum zuwa ga Allah. Ayar da aka ambata a sama, tare da hukuncin hankali tana yi mana nuni ne tana cewa: Dan Adam, wajen samun daukaka ta ruhi kamar kusanci zuwa ga Allah, kamar yadda ya kasance yana neman abin da zai biya bukatunsa na duniya, suma haka dole ne ya nemi abin da zai kusantar da shi zuwa ga wadannan abubuwan da yake bukata na ruhi, sannan ba tare da wannan ba mutum ba zai iya cimma abin da yake bukata ba.

Abin da yake akwai a nan shi ne abubuwan da suke kusantar da mutum zuwa ga Allah dole shari’a ce zata bayyana su. Domin kuwa hankalin dan Adam ba zai iya gano wadannan abubuwan ba, ta yadda zai gano abubuwan da zasu kusantar da shi zuwa ga Allah da abubuwan da zasu kai shi zuwa ga gafara da makamantansu, sannan bai kamata ba a nan wani ya yi tunanin cewa da wannan ayar ne kawai za a iya kafa hujja a kan ingancin kamun kafa da annabawa da waliyyai. Wannan aya kamar wata ka’ida ce ta baki daya wacce kuma hankali yake hukunci a kan ingancinta, amma dangane da abubuwan da zasu kusantar da mutum ko su sanya ya samu gafara ko ya samu biyan bukatunsa na ruhi, hankali ba zai iya gane wannan ba, saboda haka dole ne Allah ko manzonsa da ma’asumai (a.s) su bayyanar da hakan. Kamar yadda imam a huduba ta sama yake bayyanar da cewa imani da Allah da manzonsa da jihadi a tafarkin Allah, da tsayar da salla da bayar da zakka suna daga cikin muhimman abubuwan da suke kusantar da mutum zuwa ga Allah.

Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com – www.hikima.org – www.haidarcip.org

Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)

Facebook: Haidar Center - December, 2012



[1] -Anfal: 17.

[2] -Zukhruf: 80.



back 1 2 3 4 5 next