Kamun kafa Da Annabawa Da Waliyan Allah



Kamun kafa Da Annabawa Da Waliyan Allah

 

Mawallafi: Ayatullahi Ja’afar Subhani

Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani

Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id

Tsarin duniya yana bisa ka’idoji da dalili a kan komai, saboda haka duk wani abu wanda zai faru a duniya yakan faruwa tare da dalili wanda ya kebanci shi abin da ya farun, sannan shi ma wannan abin da ya faru zai tasiri ga wani abu na daban, tasirin da wani abu yake sanya a cikin wani daban duk yana faruwa ne da izinin Allah madaukaki. Allah shi ne wanda ya halicci duniya sannan ya sanya alaka tsakanin abubuwan da suke duniya ta yadda wasu sukan yi tasiri a cikin wasu. Babu shakka rana tana bayar da wani sinadari wanda sauran halittu suke amfani da shi don su rayu, haka nan wata yana bayar da haske, sannan wuta tana bayar da zafi. Dukkan wadannan abubuwa suna yin tasiri ga waninsu, sannan akwai alaka ta musamman tsakanin rana da wata da wuta da kuma abin da suke bayarwa. Sannan dukkan wannan tasirin da ake gani babu wanda yake sanya shi sai Allah wanda shi ne ya halicce su, sannan kuma shi ne ya sanya wannan alakar da take akwai abin da yake faruwa tsakanin abubuwa daban-daban, kuma dukkansu suna samuwa daga gare shi maudakaki. Sakamakon haka ne wani lokaci yakan dauke tasirin da abu yake da shi, kamar yadda ya dauke zafin wuta ga annabi Ibrahim (a.s) ya kuma daidaita ta tamkar wani lambu mai sanyi, wannan kuwa duk don ya nuna cewa daga gare shi ne dukkan wannan tasirin na hakika yake da kuma niyyarsa ne.

Daga wannan bayanin muna iya daukar sakamako cewa: duk wani abu wanda yake faruwa a cikin duniya muke ganinta, a lokacin da muke ganin cewa ta samu ne daga wani abu daga cikin abubuwan da suke a cikin duniya, a daida- wannan lokacin kuma suna zuwa ne daga Allah kuma aikinsa ne. Sannan wannan abin bai saba wa hankali ba ta yadda za a ce ba zai yiwuwa ba. Domin kuwa Allah shi ne wanda yake da cikakken iko yake kuma yin wani abu ba tare da taimakon wani ba, amma dukkan wani yayin da zai aikata wani abu sai da taimakon Allah. wato duk abin da suke aikatawa tare da izinin Allah suke aikata shi, don haka muna iya cewa su ne suka aikata kuma muna iya cewa Allah ne domin kuwa a hakikanin gaskiya shi ne ya aikata, domin kuwa da bai bayar da izini ba, ba za ayi hakan ba.

Sannan kowa ya san daya daga cikin matakan tauhidi ko kadaita Allah shi ne kataita Allah a cikin halitta, wato babu wani mai halittawa sai Allah madaukaki, amma duk da haka kadaita Allah a cikin halittawa ba yana nufin kore duk wani tasiri daga wani abu ba, wato ma'anarsa shi ne halitta ba tare da dogara da wani ba, shi kadai ne yake iya yin haka, sannan duk wani tasiri na sauran wasu halittu yana samuwa ne da izinin Allah.

A cikin wasu ayoyin an yi nuni da dukkan wadannan nau’o’i guda biyu na yin tasiri. Misali aiki guda a daidai lokaci guda ana a jingina shi zuwa ga Mutum, sannan kuma ana jingina shi zuwa ga Allah, duk da cewa aiki guda yana gangarowa ne kawai daga abu guda. Amma tunda wadannan masu aikin daya yana karkashin daya ne babu matsala, wato daya shi ne na asali dayan kuwa yana bin na asalin, saboda haka babu abin da zai hana hakan.

Allah yana cewa wa Manzo (s.a.w): “Ba kai ne ka yi jifa ba a lokacin da ka yi jifa”.[1] A nan Kur’ani yana jingina aiki guda daya zuwa ga masu aiki guda biyu kamar haka:



1 2 3 4 5 next