Kamun kafa Da Annabawa Da Waliyan Allah



1- Lokacin da ka yi jifa.

2- Allah ne ya yi jifar.

Dukkan wannan jinginawa guda ta yi daidai kuma ta dace da wurin, domin kuwa aikin Manzo ya faru ne da taimako da izinin Allah, saboda haka jingina wannan aiki guda daya ga dukkansu ya yi daidai. Sannan kamar aiki guda a jingina shi ga Allah sannan a jingina zuwa ga wani daban ya zo da yawa a cikin Kur’ani. Amma a nan kawai zamu bayar da misali guda biyu kawai:

1-Kur’ani a lokaci guda yana jingina rubuta ayyukan bayi zuwa ga mala’iku, [2]sannan a wani wurin daban yana jingina wannan aiki zuwa ga Allah madaukaki. [3]

2- A wani wuri ana jingina daukar rayukan mutane zuwa ga mala’ikun mutuwa, [4]amma a wani wuri ana jingina wannan aiki zuwa ga Allah.[5] Wadannan ayoyin suna bayyanar da yadda tsarin halitta yake karkashin ka’idar tasiri da mai tasiri, ta yadda abubwan da suke fauwa suke tasiri tsakanin juna. Amma dukkan wannan tsari suna jingina ne zuwa ga Allah madaukaki, sannan a karkashin nufinsa da izininsa suke ci gaba da rayuwarsu. Saboda haka duk wani abu wanda yake yin tasiri a cikin tsarin duniya, yana karkashin rundunar Ubangiji ne sannan kuma aikata abin da Allah ya umurce su ne. Sannan Allah kawai ne ya san yawan wannan runduna ta Allah. [6]

Tare da la’akari da wannan bayani, wanda yake matsayin nuni daga wahayi, (cewa babu mai halitta da gaskiya sai Allah) sakamakon binciken dan Adam na ilimi (ta yadda suka tabbatar da yadda tasirin da yake akwai tsakanin halittu a cikin duniya) ba ya nuni da sabani a kan abin da muka ambata kokadan. Wadanda suke ganin wahayi ya saba wa ilimi ko kuma addini ya sabawa ilimi, ba su yi kyakkyawar fassara ba ne a kan hakan. Ko kuma sun yi wa ilimin zamani mummunar fahimta. Da wata ma’anar kuwa, duk wadannan abubuwa guda biyu na kasa sun dace kuma sun yi daidai su ne kamar haka:

1-Imani da kadaita Allah a cikin halittawa cewa babu wani wanda yake yin wani abu ba tare da dogara da wani ba sai Allah.

2-Tasirin wasu abubuwan a cikin wasu ayyuka dukkansu suna faruwa ne da izinin Allah da nufinsa. Idan muka ga wadannan asali guda biyu wani lokaci suna karo da juna, wannan ya samu asali ne ta yadda wasu suke fassara kadaita Allah a cikin halitta da wata ma’ana wacce ba ta inganta ba. Ta yadda suke daukar babu wani mai yin wani abu sai Allah kawai, wato duk wani mai yin wani abu, ba shi yake yin abin ba, kawai Allah ne yake yin komai, dan Adam ba shi da hannu wajen yin ayyukansa (nazarin Asha’ira). Ko kuma kamar yadda wasu suke ganin bayan wadannan abubuwan da muke gani a cikin duniya suna da tasiri ga wasu abubuwa, babu wani da sunan Allah wanda yake da tasiri a cikin duniya, wato duk abin da mutum ya yi daga gareshi ne babu hannun Allah a cikin. (Nazarin wadanda ba su yarda da wani abu ba a bayan wannan duniyar da muke gani).

Saboda haka dukkan wannan fahimta guda biyu kuskure ce kuma ba ta inganta ba, wanda dukkan biyun yana nuni ne ga takaitawa da kuma wuce wuri. Rashin ingancin fahimta ta biyu kuwa ya faru ne sakamakon yadda suke ganin duniya kawai ta takaita ne ga wannan duniya da muke gani kuma muke iya jinta, wato ba su yi imani da duniyar gaibu ba, wanda ba ya bukatar wani Karin bayani. Domin kuwa a nan muna magana ne da wadanda suka yi imani da Allah kuma suna ganin rashin ingancin akidar daukar wannan duniyar ita ce kawai kuma babu wani abu a bayanta. Amma rashin ingancin fahimta ta farko kuwa yana komawa ne ga wasu daga cikin malaman akida wadanda suka tafi a kan wannan fahimta, alhali kuwa Allah madaukaki a fili yana nuna yadda halittu suke da tasiri a cikin rayuwa, wajen faruwar wasu abubuwa. Sannan kuma kowa zai iya shaida hakan domin kuwa wani abu ne wanda muke gani da idanummu.

Saboda haka ta yaya zamu ki yarda da tasirin da halittu suke da shi a cikin rayuwa, shi kuwa wahayi yana bayyana gaskiyar wannan al’amari. A matsayin misali yana bayyanar da ruwa a matsayin wanda yake da tasiri wajen rayuwar tsirrai, kamar yadda yake cewa: “Shi ne wanda ya sanya muku kasa a shimfide, sannan ya gina muku sama, Kuma yana saukar da ruwa daga sama, sannan yana fitar da ‘ya’yan itatuwa daga ruwa wadanda arziki ne a gare ku. “[7]



back 1 2 3 4 5 next