Rayuwa Bayan Mutuwa 3



6-Ibn Taimiyya (ya rasu ashekara 726) yana cewa akwai hadisai ingantattu wadanda suke nuni da dawowar rai yayin tambayar kabari.

7-Taftazani (ya rasu a shekara ta 791) yana cewa wadannan ayoyin na kasa suna nuni ga rayuwar barzahu su ne kamar:

A- “Ana bijiro wa mutanen Fir’auna da wuta a gare su safiya da yamma”.

B- “Mutanen Nuhu sakamakon laifinsu suka nutse a cikin ruwa sannan aka shigar da su cikin azaba”.

C- Ya Ubangiji ka kasha su sau biyu kuma ka rayar da mu sau biyu”.

Rayawa ta farko ita ce bayan mutuwa a cikin kabari, rayawa ta biyu kuwa ita ce bayan busa kaho. Wato; dukkan wadanda suke rayuwa a barzahu zasu rasu kafin ranar kiyama, sannan zasu rayu bayan busa kahon kiyama.

A nan mun kawo maganganun mashahuran Malaman Ahlus-Sunna dangane da wannan magana. Dangane da malaman Shi’a kuwa wannan wani abu ne wanda yake an sallama a kan ingancinsa. Sannan ya wadatar don kuwa misalin Sheikh Saduk da Sheikh Mufid duk sun rubuta wannan a cikin akidojin Shi’a.

Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com – www.hikima.org – www.haidarcip.org

Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)

Facebook: Haidar Center - December, 2012



back 1 2 3 4 5 6 7 8 next