Rayuwa Bayan Mutuwa 3



Hassan Bn Sabit ya kasance daya daga cikin mawakan wannan zamanin da aka aiko Manzo (s.a.w) wanda yake bayyanar da abubuwa ta hanyar waka a wannan lokaci, sannan ta haka ne ya kasance yana taimakon musulunci da musulmi. Sannan kuma zuwa yanzu an buga diwaninsa, sannan a cikin wannan diwani nasa ya yi magana dangane da yakin Badr a cikinta akwai bayani wannan abin da muke magana a kan shi. Ga abin da yake cewa a cikn wannan kasida ta shi:

“Lokacin da muka saka a cikin rijiya bakin dayansu, sai Manzo ya ce musu: Shin ba ku sadu da maganata ba a matsayin gaskiya, ta yadda umarnin Ubangiji yake kama har zukata. A lokacin ba su yi magana ba, da a ce zasu iya yin magana, zasu ba da amsa ne da cewa: Gaskiya abin da kake fada shi ne dai-dai.[8]

Babu wata jumla wacce tafi wannan jumla wajen bayyanar da wannan al’amariin da yake cewa: Ai ba ku fi su ji ba, sai dai su ba su iya amsawa. babu wani bayani da zai fi wannan bayyana, ta yadda Manzo ya kira daya bayan dayansu da sunansa, sannan ya yi magana da su kamar lokacin da suke a raye.

Babu wani musulmi da zai yi inkarin wannan alma’ari wanda yake a cikin tarihi saboda wata akida ta shi da ta yi rigaye, ta yadda zai iya cewa ai tunda wannan al’amari bai yi dai-dai da wannan karamin hankalin nawa ba to bai inganta ba!

Ga Matanin abin da Manzo yake cewa: Yayin da aka jefa su a cikin rijiya, sai Manzo (s.a.w) ya ce: “Ya ku ma’abuta kafirci sun kun sami abin da Allah ya yi muku alakwari da shi gaskiyane? Lallai na sami abin da Allah ya yi mini alkawari da shi gaskiya ne, sai sahabbansa suka ce masa: Ya manzon Allah kana magana ne da mutanen da suka mutu? Sai ya amsa musu da cewa: Lalli sun gane abin da Allah ya yi musu alkawari da shi gaskiya ne…”[9]

2-Lakanta wa mamaci kalamomin shahada

Lakantawa mamaci kalmomin shahada wanda muka yi maganarsa a baya, bayan nuninsa ga cewa mamaci bayan ya bar duniya yana ci gaba da rayuwa ta har abada, yana kuma nuna alakarmu da wadanda suka riga mu gidan gaskiya. Batun alakar da take akwai da wadanda suka mutu kasancewar wani abu ne bayyane, kamar yadda Bukhari yake ruwaitowa daga Anas Bn malik daga Manzo (s.a.w) cewa; wanda aka rufe yana jin karar takalman wadanda suke kai shi kabari. [10]

Sannan maganganun Abubakar da Imam Ali (a.s) zuwa ga Manzo (s.a.w) yayin da ya yi wafati yana daga cikin abin da yake tabbatar da samuwar alaka tsakanin mutum da wata duniya ta daban.

Ibn Hisham yana rubutawa a cikin littafinsa na tarihi: Lokacin da Manzo (s.a.w) ya yi wafati, abubukar ya zo a kan shinfidar mutuwarsa ya yaye abin da aka rufe fuskarsa da shi ya sumba ce shi, sannan ya ce masa: Ubana da Uwata fansa gareka, amma dangane da mutuwar da Allah ya rubuta maka yanzu ka hadu da ita, amma ba zaka sake haduwa da mutuwa ba. Sannan ya sake rufe fuskar Manzo (s.a.w)

Haka nan lokacin da Manzo ya yi wafati, bayan Imam Ali (a.s) ya yi masa wanka ga abin da yake ce masa: Ubana da uwata fansa a gareka! Tare da mutuwarka wahayi da manzanci wanda sakamakon mutuwar wani ba ya yankewa amma yanzu ya yanke. Saboda haka tunda yanzu babu shi sai mu ci gaba da hakuri wanda ka kasance kana kirammu zuwa gare shi a kan abubuwan da ba su da dadi, kamar yadda na zubar da hawaye dangane da mutuwarka har ta kasance kwalla sun bushe daga inda suke bubbugowa. Amma bakin cikimmu a kan wannan hanya zai ci gaba. Uwa da uba fansarka ya Manzo! ka kasance kana tunawa da a wata duniyar ta daban. !



back 1 2 3 4 5 6 7 8 next