Rayuwa Bayan Mutuwa 3



Rayuwa Bayan Mutuwa 3

 

Mawallafi: Ayatullahi Ja’afar Subhani

Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani

Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id

Asali Na Uku

Mun Tabbatar Da Asali Guda Biyu A Bahsoshin Da Suka Gabata

1-Hakikanin dan Adam shi ne ruhinsa.

2-Mutuwa ba shi ba ne karshen rayuwa, kawai wata kofa ce domin shiga wata duniya, sannan mutum bayan mutuwa zai rayu har abada. Sannan sai asali na uku wanda kuma ya fi sauran muhimmanci a cikin wannan Bahasi, wanda yake shi ne alakar da take akwai tsakanin rayuwar barzahu da rayuwar wannan duniyar. Domin kuwa ana iya yin tunani cewa akwai wani abu wanda ya kare mutane daga gani ko jin abin da yake faruwa a barzahu.

Idan aka tabbatar da wannan asali, zamu iya mantawa da abin da mutanen yammacin duniya suke fada dangane da al’amarin ruhi, domin kuwa mai yiwuwa ya zamana wasu abubuwan da suke fada ba a bin dogara ba ne. Kawai zamu yi Bahasi ne a kan wannan magana tare da amfani da Kur’ani da sunnar Ma’aiki da magadan Manzo (a.s).



1 2 3 4 5 6 7 8 next