Tafiya Domin Ziyarar Kabarin Manzo (s.a.w)



 Bayan dangane da ingancin wannan hadisi koda an dauki ma’ana ta farko, a akwai shakku a cikinsa. Domin kuwa yana nufin wannan Magana ta fito daga bakin Manzo inda take nuni da cewa tafiya zuwa kowane masallaci ba ta inganta sai masallatai guda uku. Alhali kuwa ruwayoyi sun zo a kan cewa Manzo (s.a.w)asu ranakun Asabar yakan tafi kasa wata sa’a bisa abin hawa domin ya je masallacin “Kuba” domin ya yi salla raka’a biyu a wajen. Wannan masallaci a zamanin da Manzo yake a raye yana da tazarar kilo mita 12 tsakaninsa da Madina.[7]

 

Ziyarar Masallatai Guda Bakwai

 A sassa daban-daban na garin Madina akwai wasu masallatai guda bakwai wadanda mahajjata sukan ziyarta yayin da suka je Madina, Idan ma muka kara da (masallacin Raddi shams, da na Bilal da na Ijaba) Yawansu zai wuce bakwai.

 Mahajjata suka yi salla raka’a biyu a wadannan masallatai musamman sukan fi ba da muhimmanci akan masallacin Imam Ali (a.s) Yanzu tambaya zata iya zuwa cewa: Idan har yin salla a wadannan masallatai ba shi da wani fifiko a kan sauran masallatai, to me ya sa mahajjata suke zuwa ziyarar wadannan masallatai sannan su yi salla a cikinsu, alhali kuwa wannan bai zo ba a cikin shari’a? Saboda haka wannan zai zama “Bidi’a” kenan a cikin addini.

 Amsar wannan tambaya kuwa a fili take:

 Tafiya domin ziyarar wadannan masallatai ba wai don ya zo a cikin shari’a ba ne, ko kuma yin salla a cikin wadannan masallatai yana da wani fifiko na musamman, sam ba haka ba ne manufar tafiya zuwa wadannan wurare sai daya daga cikin biyu ne kamar haka:

1-Tunawa da musulman farko wadanda suka kasance cikin mawuyacin halin yakin Khandak amma a cikin wannan hali ne suka gina wadannan masallatai don su yi salla kuma suka cigaba da yakinsu. Domin kuwa wasu daga cikin wadannan masallatai suna wuraren da aka gwabza tsakanin sojin tauhidi da na shirka yayin da aka kashe gwarzon shirka (Amru Bn Abdu wud) kuma sakmakon haka ne gwamnatin dagutu ta kawo karshe. Halartar musulmi a wadannan wurare tana tuna musu da wannan abubuwa da suka faru a wannan wuri. Sannan yana kara karfafa alakarsu da wadanacan musulman farko.

2-Amma ma’ana ta biyu kuwa da zata iya zama dalilin da ya sa musulmai suke zuwa wadannan masallatai ita ce, domin neman tabarraki daga wadannan wurare, domin jinanan shahidai a kan hanyar tauhidi a wadannan wurare ne ya zube, Saboda haka wannan wurare sun sheda kai da kawon shahidan musulunci, sannan kuma wuri na kai-da-kawon manyan musulmai.

 Wadannan manufofi su ne suke sanya musulmi suna tafiya zuwa wadannan wurare da makamantansu, kamar wurin da aka yi yakin khaibar da Fadak, duk sun samo asali ne daga wadannan manufofi guda biyu.



back 1 2 3 4 5 6 7 next