Tafiya Domin Ziyarar Kabarin Manzo (s.a.w)



2-Ana yin tafiya ne kawai zuwa ga masallatai guda uku.[6]

Ibn taimiyya ya yi riko ne da zahirin wannan hadisi domin tabbatar da manufarsa, ta yadda ya yi da’awar cewa domin aiwatar da ayyukan ibada masallatai uku ne kawai mutum zai iya zuwa domin yin hakan. Saboda haka ziyarar Manzo wanda yake matsayin ibada ba ya daya daga cikin wadannan abubuwa guda uku.

Wannan kafa hujja ta Ibn Taimiyya kuwa idan muka lura da kayu zamu iya gane rashsin ingancinsa, domin kuwa ba shi da kafafuwa masu karfi.

 Domin kuwa mun san cewa jumlar da take kebewa tana ginuwa daga sassa guda biyu kamar haka:

1-Jumlar da ake kebewa daga gareta: “Ba wanda ya zo wurina”

2- Jumlar da a ka kebance “Sai Ali”

Hadisin da ya gabata ya ginu ne ta hanyar jumloli biyu ne.

1-jumla ta farko jumlar da aka kebance daga gare ta “Kada ku yi tafiya”.

2-Jumla ta biyu kuwa, wadda a ka kebance. “Sai masallatai uku”.

A jumlar ta farko abin da aka kebance bai fito ba a fili, bisa la’akari da ka’dar larabci a nan dole mu kadda wata jumla, wadda zata iya zama daya daga cikin wadannan jumloli guda biyu kamar haka:



back 1 2 3 4 5 6 7 next