Bidi’a A Cikin Addini



Amma masana suna bayyanar da ma’anar bidi’a kamar haka:

A-Bidi’a ita ce kari ko rage wani abu a cikin addini, sannan a dauki wannan abin daya daga cikin addini.[8]

B-Bidi’a ita ce kawo wani abu sabo a cikin addini alhali babu dalilin shari’a a kan halarcinsa. Amma idan wannan kawo sabon abin yana da asali a cikin shari’a to ba ‘bidi’a’ ba ce.[9]

C-Bidi’a ita ce farar da wani abu sabo a cikin addini. Tare sharadin cewa babu wani dalili ko asali daga addini da yake nuna halascin abin, ana kiran wannan bidi’a a cikin addini a tsakanin musulmi[10].

Muna iya wadatuwa da wadannan ma’anoni guda uku. Sannan mu manta da sauran ma’anonin da ba su da ma wani muhimmin bambanci da wadannan. Saboda haka daga wadannan ma’anoni zamu iya fahimtar cewa bidi’a tana da wasu rukunnai guda uku wadanda suke raba ta da ‘Sunna’.

 

1-Sanya wani abu a cikin addini

Duk wani kari ko ragi a cikin addini wanda zai sanya addini ya samu wani canji sakamakon hakan, sannan kuma a danganta wannan zuwa ga Allah ko manzonsa. Amma sabunta wani abu wanda zai sanya mutum ya samu wani canji a ruhinsa, ba a kiransa bidi’a. Amma mai yiwuwa ya kasance bai halatta ba amma ba a kiran sa bidi’a da wannan ma’anar.

Daga wannannan bayani zamu iya fahimtar cewa akwai wasu ayyuka daga cikin ayyukammu wadanda mai yiwuwa su zama halas ko haram, amma ba a kiransu bidi’a, kamar misalin kwallon kafa ko wani nau’i na wasanni. Irin wadannan sababbin abuwa a cikin rayuwa, sakamkon kasantuwarsu ba shigar da wani abu ba ne a cikin addini ba a kiransu da bidi’a.

A yau ga wadanda suka samu tasiri daga turawa al’adar hada maza da mata a taruka wani abu wanda ya zama ruwan dare, amma tunda masu yin wannan aiki ba su danganta shi zuwa ga Allah ba, don haka ba a kiran wannan bidi’a, duk da cewa a mahangar musulunci ya haramta.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 next