Hakkin Rai



Amma masu yarda da wani abun bayan mariskai, wanda muke cewa da su "bajiki" kamar ran dan Adam da ba a iya riskarta da mariskai wasu sun tafi a kan cewa mutum shi ne kawai ransa da aka fi sani da hakikar zatinsa. Sai dai Sadrul Muta'allihin wanda muka fi gamsuwa da nazarinsa yana ganin mutum shi ne duka biyu, sai dai yana da darajoji da marhaloli; daraja mafi girma ita ce ransa, daraja mafi karanta shi ne jikinta, kuma dukkanin wannan shi ne ya hada mutum.

Kuma da wadannan bayanai ne zamu iya samun amsar mene ne hakikanin mutum, kuma da can akwai rai tun kafin duniya ko kuwa? Sannan shin idan mutum ya mutu ransa tana lalacewa ne kamar yadda jikinsa yake lalacewa ko kuwa? Kuma a wannan duniyar mene ne zamu karfafa jiki ne ko rai ko duka biyu? Meye idan ya gyaru komai zai gyaru shin da yin ado ne na zahirin jiki, ko kuma ta hanyar tsarkake badinin da muka sanya wa suna da “bajiki” kamar rai? Kuma yaya dan Adam zai samu kamalar da yake burinta a wannan duniyar ta yadda wannan duniyar zata zamanto tamkar wani dausayin aljanna mai ni’ima gareshi? Kuma yaya za a iya kawo gyara a cikin al’ummu? Sannan yaya muka ga wasu mutane sun fi wasu karfin zati, ta yadda darajojinsu suka sassaba? Dukkan irin wadannan tambayoyi masu amsuwa ne cikin sauki idan muka dauki nazarin musulunci kan rai da rayuwar mutum.

Amma wadanda suka yi musun Allah suka ki yarda da samuwar badini da abin da yake bajiki ne kamar ‘yan nazarin mariskai ko masu nazarin “Zahirin samuwa”, kamar ‘yan Kwaminis, ba zasu iya cewa komai ba game da wannan tambayoyi. A fili yake muna gani ba zasu iya ba wa dan Adam mafita ba a rayuwarsa ta duniya ta zahiri wacce suke hankoron cimma ta, suke ta wahala a kan samun ta, balle kuma su ba shi mafita kan lamarin badinin rayuwarsa da ta shafi ransa da zatinsa al’amarin da su ba su yi imani das hi ba.

Sannan rai ita ce take da karfi kan bangaren jiki, muna iya cewa jiki sandararre ba shi da wani abu da zai iya yi sai abin da rai ta ba shi umarni, sai dai shi ma yana tasiri a kanta ta fuskacin rashin lafiyarsa. Idan jiki ba shi da lafiya to yakan ki umarnin da rai take bayarwa, kamar rai tana kwararo masa tunani, sai ya kasance akwai jini a kwakwalwarsa sai ya haukace, to wannan umarnin ba zai aiwato ba, zai koma sururi ne kawai, haka ma bangaren makanta idan ido ya samu matsala, ko ji idan kunne ya samu matsala.

Rai tana tafiyar da jiki, tana ba shi umarni mai kyau, don haka ne ake son jiki ya kasance mai lafiya, domin a samu sakamako mai kyau na umarnin da rai take bayarwa. Idan jiki yana da lafiya sai a samu nishadi, sai umarnin rai ya aiwatu, idan ba haka ba kamar ga maras lafiya, ransa tana iya son ya tashi ya yi salla amma sai ya kasa. Masu hikima sukan ce: Hankali mai lafiya cikin jiki mai lafiya[10].

Alakar rai da jiki alaka ce mai karfi da ta yi kama da alakar jini da tsoka ko sama da haka, sannan wannan alakar ta yi wuyar sani ga masu bincike, don haka ne da yawan masana suka sallama wa wannan lamarin zuwa ga mahaliccin duka, sai kuma wadanda suke daraja masana da izinin Allah kamar manzon rahama (s.a.w) da wasiyyansa (a.s).

Masana sun yi sabani kan ita kanta rai din mutum cewa shin jiki ce mai taushi kamar iska da aljani, sai dai ba za a iya riskarta da mariskai na zahiri kamar gani ko jini, ko tabawa ba. Ko kuwa rai wani abu ne da yake bajiki ta yadda babu wata hanyar da mariskai na zahiri zasu iya riskarta atafau. Sai malaman akida suka tafi a kan cewa ita jiki ce mai laushi da taushi da ma'anar da muka kawo kamar jikin aljani, ko iska, malaman Falsafa kuwa suka tafi a kan magana ta biyu cewa rai bajiki ce, don haka babu wata hanyar da za a iya riskarta.

Kamar yadda aka yi sabani kan yadda take sarrafa jiki, shin tana cikin jiki ne ko wajen jiki take, sai masu gani ta a matsayin jiki ce kuma suna ganin ta a matsayin wani bangare ne na jiki suka dauka cewa tana cikin jiki ne. Amma masana masu zurfafawa sai suka tafi a kan cewa ita rai wani abu ne mai sarrafa jiki da yake tare da shi, sai dai ba kamar ruwa cikin kwano ba, ko kamar wani bangare cikin wani abu ba.

Sannan wannan alakar ta rai da jiki ba abu ne mai saukin warware ko rabuwa ba ne, alaka ce mai karfi matukar gaske. Kamar dai alakar mai aiki da yake sana'anta wani abu da kayan aikinsa, ta yadda idan babu wadannan kayan aikin ba wani abu da zai iya yi, kamar makeri ne da idan babu guduwa da sauran kayan aiki ba abin da zai iya, ko dan fawa da wuka, ko mai noma da fatanya, ko mai rini da kayan rini.

Haka nan rai take amfani da wadannan bangarori na jiki cikin sauki da kuma sauri maras iyaka, sai ta ji, ta gani, ta fahimta, ta shaka, da taba, ta dandana, duk da wadannan kayan aikin nata da suka hada da fatar jiki, da ido, da kunne, da harshe, da sauransu. Kamar yadda take aiwatar da fasahohi da wannan jiki, sai ta yi wasanni, ta yi kirar abubuwan more rayuwa, ta yi sakar tufafi da tunanin da ta suranta, kuma ta bayar da umarni ga jiki da gabobi su aiwatar da shi.



back 1 2 3 4 5 6 next